Daga ran 8 zuwa ran 15 ga wannan wata, bisa gayyatar da aka yi masa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyarar aiki a kasar Britaniya da Jamus da Spain. Wannan ne wani babban aikin diplomasiya da shugaban koli na kasar Sin ya yi a shiyyar kasashen Turai bisa halin da ake ciki a yanzu . An ce, ziyarar da Mr Hu Jintao ya yi a wannan gami ta ci burin da aka tsara, kuma ta sami cikakkiyar nasara.
Bisa ka'idar kara wa juna fahimta da kara samun ra'ayi daya da hanzarta hadin guiwa da kara wa juna zumunci ne, Mr Hu Jintao da shugabannin kasashen uku da yake ziyara suka yi musayar ra'ayoyinsu a kan matsalolin da suka jawo hankulansu duka da huldar da ke tsakanin bangaorrin biyu, Mr Hu Jintao ya kuma gana da mutane na rukunoni daban daban da kuma ya shawo kan bangarori daban daban a kan wasu abubuwa da kuma bayyana ra'ayin kasar Sin a kan raya kasa cikin lumana da sauran manufofinta. Game da sakamakon da aka samu a gun ziyarar, shguaban sashen kula da harkokin kasashen Turai na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Zhao Jun ya bayyana cewa, ziyarar ta kara zurfafa da kuma kara inganta huldar siyasa da ke tsakanin bangaorin biyu da kuma hanzarta hadin guiwar aiwatar da hakikanin aiki wajen tattalin arziki da cinikayya, a sa'I daya kuma, ta kara inganta tushen yin hadin guiwa da zumunci da ke tsakanin bangarorin biyu da kuma tabbatar da makomar bunkasa huldar da ke tsakanin bangarorin biyu da hanzarta bunkasuwar huldar abokantaka da ke tsakanin kasar Sin da wadannan kasashen uku da kawancen kasashen Turai bisa manyan tsare-tsare a dukan fannoni. A duk tsawon lokacin ziyarar, kasar Sin da wadannan kasashen uku sun daddale wasu yarjejeniyoyin hadin guiwa masu muhimmanci da kwangiloli da yawa. Ziyarar ta ci burin da aka tsara kuma ta sami cikakiyyar nasara.
Bunkasa huldar da ke tsakanin kasar Sin da kawancen kasashen Turai da kasashen Turai wani muhimmin kashi ne da ke cikin manufar diplomasiya ta kasar Sin. Mr Zhao Jun ya bayyana cewa, nasarar da Mr Hu Jintao ya samu a gun ziyarar da ya yi a kasar Britaniya da Jamus da Spain ta bayyana cewa, huldar da ke tsakanin kasashen Turai da kasar Sin ta jure lokaci da sauyawar al'amuran kasashen duniya, ta riga ta shiga matakin samun bunkasuwa cikin zaman karko. Yanzu, manyan shugabannin bangarorin biyu suna ta kai wa juna ziyara da kuma yin tattaunawa da shawarwari a tsakaninsu, kuma huldar da ke tsakaninsu wajen tattalin arziki da cinikayya tana kara samun bunkasuwa, mutanensu kuma suna yin cudanya sosai da dai sauransu. Hadin guiwar da ke tsakaninsu yana kasancewa tun tun tuni, kuma na da boyayyen karfi da za a iya yin amfani da shi. Saboda haka, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai tana samun dama mai kyau wajen ci gaba da samun bunkasuwa. Mr Zhao Jun ya bayyana cewa, da farko, kasar Sin da kasashen Turai suna iya taimaka wa juna a fannoni da yawa, na biyu, bangarorin biyu suna da moriya daya wajen kiyaye zaman lafiya na duniya da tsaron kai da kuma sa kaimi ga samun bunkasuwa a tsakaninsu, na uku, bangarorin biyu dukansu suna da dogon tarihi da wayin kai wajen fannoni da yawa sosai.
A lokacin da ake bunkasa huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, bangarorin biyu suna da bambancin ra'ayi a tsakaninsu, wannan mai abu ne da ba a iya kawar da shi ba.
Mr Zhao Jun ya bayyana cewa, kara bunkasa huldar abokantaka da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ta hanyar bude wa juna kofa da aiwartar da hakikanin aiki ba tare da yin adawa da bangare na uku ba bisa manyan tsare-tsare a dukan fannoni ya dace da gundanarwar samun bunkasuwa na duniya da babbar moriyar jama'ar kasashe daban daban.(Halima)
|