Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-16 16:01:51    
Wakilan bangaren siyasa da na kasuwanci na Sin da Amurka sun yi tattaunawa a birnin Beijing

cri
Hulda da ke tsakanin kasar Sin da Amurka tana daya daga cikin hulda mafi muhimmanci a tsakanin kasashe biyu a duniya, sabili da haka ba ma kawai yalwatuwar huldar nan tana jawo hankulan kusoshin kasashen nan biyu ba, har ma mutanen bangarori daban daban su ma suna ta yin kokari sosai wajen ciyar da huldar nan gaba. A gabannin ranar da W. Bush, shugaban kasar Amurka zai soma ziyara a kasar Sin, an yi taron tattaunawa na karo na biyu a kan huldar da ke tsakanin Sin da Amurka a nan birnin Beijing ran 14 ga wata. Wakilan manyan mutane da na masanan ilmi da 'yan kasuwa na kasashen biyu sun yi tattaunawa mai zurfi a kan yin ciniki tsakanin kasashen biyu cikin daidaituwa da rikicin cinikin kayayyakin saka da aikin kare ikon mallakar ilmi da kuma sauran matsaloli masu muhimmanci ga huldar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma sun sami ra'ayi bai daya a kan kara karfin hadin guiwar kasashen biyu a fannoni daban daban.

Bayan da Mr George Bush, tsohon shugaban kasar Amurka wanda ya gabatar da shawara kan yin tattaunawar ya nuna babban yabo ga ci gaba da aka samu wajen yalwata hulda da ke tsakanin Sin da Amurka, sai ya tabo magana a kan ziyarar da dansa George Walker Bush, shugaban kasar Amurka zai fara yi a kasar Sin a ran 19 ga wata. Ya ce, "babban dana Bush zai yi ziyara a kasar Sin nan gaba kadan, yana nuna wa kasar Sin babban aminci, kuma yana dora matukar muhimmanci ga hulda da ke tsakanin Sin da Amurka. A ganinsa, huldar nan tana da kyaun gaske har ba a taba ganin irinta ba a da, amma kamata ya yi a kara kyautata ta. Huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta sami manyan sauye-sauye a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, dukammu muna ganin cewsa, huldar nan tana daya daga cikin hulda mafi muhimmanci a duniya. A ganina, kasar Amurka tana fatan ganin kasar Sin wata kasa ce mai zaman karko da wadatuwa da makwabtanta."

An sami ci gaba da sauri wajen bunkasa harkokin ciniki tsakanin Sin da Amurka a cikin shekarun nan da suka gabata. Amma wasu mutanen Amurka sun nuna damuwa ga gibin kudi da Amurka ta samu daga wajen ciniki da take yi tare da kasar Sin, amma Mr David A. Sampson, mataimakin ministan kasuwanci na Amurka ba haka yake gani ba. Ya ce, "yanzu mutane su kan tabo magana a kan gibin kudi da Amurka ta samu daga wajen ciniki da take yi tare da kasar Sin, amma ba su lura da harkokin ciniki da kamfanonin Amurka ke yi a kasar Sin ba. Muna samun gibin kudi daga wajen ciniki da muke yi tare da Jamus da Japan, amma harkokin tattalin arzikin kasar Amurka na bunkasuwa, sabo da haka ba daidai ba ne a lura da gibin kudin nan da ake samu kawai. Daga binciken da aka yi kwanakin baya a kan matsakaicin yawan kudin riba da kamfanonin Amurka suka samu a kasar Sin, an gano cewa, a ganin kashi 2 bisa kashi uku na kamfanonin nan, yawan kudin riba da suka samu a shekarar bara ya karu, kuma zai kara karuwa a shekarar nan. "

A kwanakin baya, an daddale yarjejeniya game da kayayyakin saka a tsakanin Sin da Amurka. Da Malam Liao Xiaoqi, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya tabo magana a kan yarjejeniyar, sai ya bayyana cewa, "yin shawarwari kan kayayyakin saka tsakanin Sin da Amurka abu ne mai kyau ga duk kasashen nan biyu, abin da ya fi muhimmanci shi ne samar da guraben ciniki masu karko ga masu cinikin kayayyakin saka na kasashen biyu. Amma ba mu son ganin yawan kayayyakin saka da aka kayyadde wajen yin cinikinsu, dalilin da ya sa haka shi ne domin bai kamata a yi haka ba yayin da ake samun haduwar tattalin arzikin duniya ko kuma ba da 'yancin yin ciniki." (Halilu)