A ran 13 ga wannan wata wajen karfe 2 na rana, an yi ta samun fashe fashe a wata ma'aikatar sarrafa magunguna ta lardin Jilin da ke arewacin kasar Sin. Ya zuwa yanzu, mutum daya ya mutu a yayin da mutane biyar suka bace tare da mutane 70 da suka ji raunuka bisa sanadiyar fashe fashen da aka samu. Yanzu, an riga an shawo kan gobarar sosai, jama'ar da suka warwatse zuwa sauran wurare sun riga sun soma komawa gidajensu, aikin daidaita hadarin yana nan yana tafiya yadda ya kamata.
Lokacin da ma'akatar ta sami labarin fashewar, a wuraren da ke nesa da ma'aikatar da kilomita dari ko dari biyu, an lalace dukan gilashin tagogin gidajen wurin. Bisa abubuwan da wadanda suka ganam ma hadarin da idonsu suka bayyana, an ce, an ji kararrakin fashewar har sau biyar ko shida.
Bayan aukuwar hadarin, sassan da abin ya shafa na wurin sun soma aiwatar da shirin ko ta kwana na magance hadarin cikin gaggawa, sun yi iyakacin kokari don aiwatar da aikin magance al'amarin, wani jami'in birnin Jilin na lardin Jilin mai suna Qiao Zhengchong ya gaya wa manema labaru abubuwa dangane da yadda ake aiwatar da aikin magance al'amarin. Ya bayyana cewa, bayan aukuwar al'amarin, mun dauki matakai guda uku, na farko shi ne, yin aikin ceto a wurin da hadarin ya faru da kuma hana kara tashin gobara da tsananta al'amarin, na biyu, mun janye mutanen da ke kewayen wurin, amma yanzu, wato na uku , muna nan muna soma aikin cigiyar da wadanda suka ji raunuka domin cetonsu.
Bayan fashewar da aka samu, an janye dalibai na wasu makarantu da mazauna fiye da dubu goma da ke kewayen wurin nan. An kai wadanda suka ji raunuka cikin asibitoci guda biyu na wurin, an riga an yi wa wadanda suka ji raunuka masu tsanani guda biyu tiyata , ga alamar, yanzu, ba za su gamu da hadarin rasa rayuka ba.
Mun sami labari daga wajen taron bayar da labarai da aka kira a tsakar daren ranar da hadarin ya faru cewa, an riga an gano sanadiyar aukuwar hadarin, wato ba a daidaita cikas da aka samu a lokacin da wata na'urar ma'aikatar sarrafa magunguna take aiki ba tare matsala ba. Muhimman kayayyakin da suka haifar da tashin gobara su ne danyun kayayyaki da ake kira "benzene" cikin Turanci. Yanzu, an riga an kashe gobarar. Mataimakin manajan kamfanin sarrafa magunguna na lardin Jilin Zou Haifeng ya bayyana cewa, yanzu, sassan da abin ya shafa sun riga sun soma bincike kan kazamtar da aka yi wa yanayin sararin samaniya, sakamakon da aka samu ya bayyana cewa, an riga an juya halin da wurin ke ciki na kasancewar iska maras kyau, kuma babu kwayoyin guba da zai sa mutane za su sha. Ya bayyana cewa, bisa bayanan da kwararrun kiyaye muhallin hallita da tsaron lafiya da kwararrun yin rigakafi da magance ciwace-ciwacen da aka kamu da su bisa sanadiyar aikinsu, an bayyana cewa, kafin konewarsa, abin da ake kira ""benzene" yana da guba sosai, amma bayan fashewarsa tare da gobara, sai nan da nan ya zama ruwa da "carbon dioxide" da "carbon Black" wadanda ba su iya sanya mutane shan gubar ba. Mun riga mun aiwatar da shirin ko ta kwana cikin gaggawa, kuma a daidai lokaci ne muka yi bincike kan iskar da ke wurin ma'aikatar da wuraren da mazauna ke zama , an gano cewa, ba a gano iska mai guba ba.
Yanzu, mutanen da aka janye su sun riga sun koma gidajensu, kuma makarantun da aka rufe su ma sun yi shirin bude kofofinsu a ran 14 ga wannan wata da yamma.(Halima)
|