A ran 8 ga watan nan a London, kasar Sin da kasar Amurka sun sa hannu kan " Takarda game da cinikin kayayyakin saka da tufafi." A cikin takardar nan bangarorin biyu sun tanada cewa, a shekaru 3 masu zuwa za a kuntata karuwar kayayyakin saka iri 21 da kasar Sin ke fitarwa kasar Amurka cikin kashi 10 cikin kashi 100 zuwa kashi 17 cikin kashi 100. masanan ilmin tattalin arziki da masu sana'ar saka na cikin gidan kasar Sin sun yi yabo ga sayon din yarjejeniyar nan. A ganinsu wannan takarda za ta tabbatar da muhallin ciniki mai dorewa ga masana'antu na kasashen biyu. Yanzu sai ku saurari labarin da aka ruwaito mana.
A ran 8 ga watan nan, Bu Xilai, ministan ciniki na kasar Sin da Portman, wakilin ciniki na kasar Amurka, a makwafin gwamnatinsu ne suka sa hannu kan " Takarda game da cinikin kayayyakin saka da tufafi." Sabo da haka an sa aya ga gardamar cinikin kayayyakin saka da Sin da Amurka suka yi har dogon lokaci.
Bo Xilai, ministan ciniki na kasar Sin ya ce, Sin da Amurka sun sa hannu kan wannan takarda, wannan nasara ce ga kowa, amma kuma ya bayyana cewa, ya kamata kasashe masu sukuni su gane cewa, bai kamata ba su kuntata yawan kayayyakin saka da a ke ciniki.
Bangarori biyu wato Sin da Amurka duk sun ji dadi da takardar da aka sa hannu. Mr. Song Hong, mai binciken tattalin arziki da siyasa na duniya na kolejin kimiyar zaman al'umma na kasar Sin ya bayyana cewa, Bangaren Amurka ya yi rangwame kan karuwar cikin kayayyakin saka. Da ma ta tsaya kan karuwar cinikin kayayyakin saka na kashi 7.5 cikin kashi 100, amma yanzu ya kai kashi 10 cikin 100 zuwa kashi 17 cikin kashi 100. kasar Sin kuma ta yi rangwame kan tsawon lokaci, wato da ma har zuwa shekara ta 2007 ne , amma yanzu har zuwa shekara ta 2008 ne. kan irin kayayyakin saka da za a yi ciniki ma kasar Sin ta yi rangwame, da ma ta yarda da za a kuntata kayayyakin saka iri 10 ne. sabo da haka, bangarorin biyu duk sun yi rangwame.
Bayan da kasar Sin da kasar Amurka suka sa kannu kan yarjejeniya kan gardamar cinikin kayayyakin saka, sana'ar kayayyakin saka ta kasar Sin ma ta nuna maraba. Mr. Sun Huibing, kakakin kungiyar masaku ta kasar Sin ya ce, Ko da ya ke wannan takarda ta kuntata yawan kayayyakin saka da za a yi ciniki bayan da bangarorin biyu suka yi shawarwari, amma ta kago wani muhallin ciniki mai dorewa a shekaru 3 masu zuwa wato daga shekara ta 2006 zuwa shekara ta 2008.
Sun Huaibing ya nuna cewa, ko da ya ke kasar Sin ta kulla yarjejeniya da Amurka da Turai, amma mai yiwuwa ne gardamar ciniki za ta tashi. Sabo da haka, ya kamata sana'ar saka ta kasar Sin ta yi kokarin kara kwarewar aikinsu don kara karfin gasa. (Dogonyaro)
|