Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-09 17:50:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(3/11-9/11)

cri
Ran 6 ga wata da dare, an rufe wasannin motsa jiki na karo na 4 na gabashin Asiya a Macao, yankin musamman na kasar Sin. Kungiyar wakilai ta kasar Sin ta sami lambobin zinariya 127 a gun wasannin nan, wato ke nan yawan lambobin zinariya da ta samu su ne mafi yawa? kungiyar wakilai ta Japan ke biye mata, haka nan kuma kungiyar wakilai ta kasar Korea ta Kudu ta zo ta uku. 'Yan wasa sama da 3000 wadanda suka fito daga kasashe da shiyyoyi 9 ne suka shiga cikin wasannin nan. A kan shirya wasannin nan ne a ko wadanne shekaru 4, za a shirya wasannin motsa jiki na karo na biyar na gabashin Asiya ne a Hong Kong, yankin musamman na kasar Sin a shekarar 2009.

An shirya gagarumin biki a Hong Kong a ran 6 ga wata don yin maraba da tutar wasannin motsa jiki na gabashin Asiya da wutar tocila. Gwamna Donald Tsang na Hong Kong ya bayyana a gun bikin nan cewa, gwamnatin Hong Kong za ta nuna cikakken goyon bayanta ga bangaren wasannin motsa jiki da sauran bangarori na Hong Kong don samun sakamako mai kyau wajen shirya wasannin motsa jiki na karo na biyar na gabashin Asiya a Hong Kong a shekarar 2009 wanda ba a taba ganin irinsa ba a da.

A cikin karawar karshe ta gasar wasan kwallon kafa ta maza ta wasannin motsa jiki na karo na hudu na gabashin Asiya da aka shirya a Macao na kasar Sin a ran 6 ga wata da dare, kungiyar maza 'yan wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta lashe ta kasar Korea ta Arewa da ci 1 da ba ko daya, inda ta zama zakara. Wannan karo ne na farko da kungiyar maza 'yan wasan kwallon kafa ta Sin ta zama zakara a cikin irin wadannan wasannin motsa jiki da aka yi a shekarun nan da suka wuce.

A ran 11 ga wannan wata, za a gabatar da alamar fatan alheri ta wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Kwamitin kuila da harkokin shirya wasannin Olympic ta Beijing za ta shirya bikin kaddamar da alamar fatan alheri a baban dakin wasan motsa jiki ta ma'aikatan Beijing a daren wannan rana. Bisa wani labarin daban da aka bayar, an ce, an yi cikakken zaman taro na 5 na kwamitin daidaituwa ta wasannin Olympic ta Beijing ta hukumar wasannin Olympic ta kasa da kasa a birnin Beijing a ran 8 ga wata. A gun taron nan, an yi tattaunawa a kan yadda za a gudanar da filayan wasa da dakunan wasa da harkokin kasuwanci da sayar da tikitoci da ba da tocilar wasan da dai sauransu a lokacin wasannan Olympic na Beijing.

A ran 6 ga wata, an rufe budaddiyar gasar wasan badamindo ta Hong Kong ta shekarar 2005. Bayan da dan wasa Lin Dan na kasar Sin ya zama zakara a cikin gasar tsakanin maza zalla, 'yar wasa Zhang Ning ta kasar Sin ta zama lambawan a cikin gasar tsakanin mata zalla, 'dan wasa Xie Zhongbo da 'yar wasa Zhang Yawen sun zama zakaru a cikin gasar tsakanin gaurayar maza da mata, sai Yang Wiei da Zhang Jiewen sun zama zakaru a cikin gasar tsakanin mata bibbiyu, Fu Haifeng da Cai Yun su ma sun zama zakaru a cikin gasar tsakanin maza bibbiyu. Ta haka dai ne 'yan wasa na kasar Sin suka zama zakaru biyar na duk gasar nan, wannan sakamako ne mafi kyau da 'yan wasa na kasar Sin suka samu a cikin irin wannan gasar wasan badamindo da suka taba shiga tun daga shekarar 1982 har zuwa yanzu.

Ran 6 ga wata, an kawo karshen budaddiyar gasar wasan judo ta Finland ta shekarar 2005 wadda aka shafe kwanaki biyu ana yinta a kasar Finland. Kungiyar kasar Sin ta sami lambobin zinariya guda uku a cikin gasar nan. Kimanin 'yan wasa 250 wadanda suka fito daga kasashe da shiyyoyi 23 ne suka shiga budaddiyar gasar nan.

Ran 7 ga wata, an sa aya ga karawar karshe ta gasar ba da babbar kyauta ta tsaren motoci ta A1 a birnin Sydney na kasar Australiya. Yawan ayarin motoci da suka shiga cikin gasar nan ya kai 24. Sakamakon gasar nan shi ne Ayarin motoci ta kasar Faransa ta zama zakara, ayarin Britaniya ke biye mata, ayarin kasar Switzerland kuma ta zo ta uku. (Halilu)