Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-09 17:26:36    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya fara ziyarar aiki a kasashe hudu na Turai da Asiya

cri

A ran 8 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga birnin Bejing domin fara ziyararsa a kasashen Ingila da Jamus da Spain da Korea ta kudu bisa gayyatar da suka yi masa, haka kuma shugaba Hu zai halarci kwarya-kwaryar taro na 13 a tsakanin shugabannin kasashen kungiyar APEC da za a shirya a birnin Pusan na kasar Korea ta kudu. Wannan ziyara kuma za ta shafe kwanaki 12 yana yinta. Ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya bayyana cewa, wannan ziyarar da shugaba Hu yake yi za ta taka wata muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bungasuwar dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen hudu da kuma bunkasuwar kungiyar APEC.

Kasashen Ingila da Jamus da Spain da Korea ta kudu kasashe ne masu ci gaba a fannin tattalin arziki, haka kuma su ne kasashe da ke iya bayar da muhimmin tasiri a yankuna daban daban har a duk duniya. A 'yan shekarun baya, danganta tsakanin kasar Sin da kasashen hudu na bunkasuwa cikin sauri, haka kuma suna kara hadin kansu a fannoni daban daban. A gun wani taron manema labaru da aka shirya, Li Zhaoxing ya bayyana makasudin ziyarar da shugaba Hu ya yi a kasashen hudu. Ya ce, 'Makasudin wannan ziyara shi ne kara amincewar juna da samun ra'ayi daya da kuma kara sa kaimi ga hadin kai da zumunci a tsakaninsu. Shugba Hu zai gana da shugabannin kasashen hudu da sauran mutane na fannoni daban daban inda za su tattauna yadda za su hada kansu da kara yin mu'amala da juna a fannoni daban daban. Ban da wannan kuma, shugaba Hu zai bayar da jawabai a wasu muhimman wurare domin bayyana hanyar bunkasuwa da kasar Sin ke bi cikin lamuna da manufofinta kan sauran batutuwa.'

Tun bayan da kasashen Sin da Ingila suka kafa dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare a fannonin daban daban a shekarar 2004, dangantakarsu ta kara bunkasuwa cikin sauri: shugabannin kasashen biyu suna ta ganawa da juna da yin mu'amala da juna, bangarorin biyu suna samun nasarori da yawa a kan hadin kansu a fannonin ciniki da zuba jari da sha'anin kudi da makamashi da kimiyya da fasaha da aikin ba da ilmi da kiyaye muhalli da dai sauransu. Wannan ziyara ta zama ziyarar aiki ta farko da shugaban kasar Sin ya kai wa kasar Ingila. Ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya ce, 'Wannan ziyarar ta shugaba Hu za ta kara amincewar juna a tsakanin bangarorin biyu, haka kuma za ta kara habaka hadin kai da suke yi a halin yanzu.'

Kasar Jamus ta kasance kasa ta farko a Turai kuma ta biyu a duk duniya a kan cinikayya, haka kuma ta zama kasa ta uku a duk duniya a kan tattalin arziki. Dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da ta Jamus na bunkasuwa da kyau, ba kawai kasashen biyu suka hadin kai a fannonin tattalin arziki da aikin ba da ilmi da kimiyya da fasaha da kiyaye muhalli da shari'a ba, har ma suna yin mu'amala da hadin kai a al'amuran shiyya shiyya da na duniya. A 'yan kwanakin da suka gabata ba da dadewa ba, an yi babban zaben shugaban kasar Jamus, sabo da haka, dangantakar tsakanin Sin da kasar Jamus tana fuskantar wata sabuwar dama. Li Zhaoxing yana ganin cewa, wannan ziyarar da shugaba Hu yake yi a kasar Jamus za ta zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu.

Dangantar da ke tsakanin kasar Sin da Spain tana bunkasuwa lami lafiya, wadda kuma take kara samar wa jama'arsu moriya mai yawa. Li Zhaoxing ya yi imani da cewa, ziyarar za ta kara daga matsayin dangantakarsu a tsakanin kasashen biyu, dangantakar za ta shiga cikin wani sabon wa'adi.

Kasar Korea muhimmiyar makwabciyar kasar Sin ne kuma kawarta. A 'yan shekarun baya, dangantakar abokantaka a fannoni daban daban tana bunkasuwa cikin sauri. Haka kuma bangarorin biyu suna ta yin mu'amala da hadin kai da kyau a kan batun nukiliya na zirin Korea da yin gyare-gyaren MDD da dai sauransu.

Kungiyar APEC wata muhimmiyar kungiya ce a yankin Asiya da tekun Pacific, kasar Sin tana fata kasashen kungiyar za su kara hada kansu. Li Zhaoxing ya ce, 'Shugaba Hu zai bayyana ra'ayoyin kasar Sin a kan sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a duk duniya cikin dogon lokaci da shawararta game da kungiyar APEC, haka kuma zai yi kira da a hada kai domin rigakafin sababbin cututtuka. Ban da wadannan kuma shugaba Hu zai bayyana hanyar da kasar Sin za ta bi wajen bunkasa tattalin arziki da dai sauran batutuwa.'(Danladi)