Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-04 10:37:28    
Gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da wani shirin taimakon nakasasu marayu wajen samun magani

cri
Gwamnatin kasar Sin tana nan tana tafiyar da wani shirin taimakon nakasassu marayu wajen samun magani.A cikin shekara sama da daya tun da aka aiwatar da shirin nan,nakasassu marayu fiye da 9100 sun sami taimako wajen samun magani. A ran biyu ga wata ,Mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin Li Liguo ya fayyace cewa kimanin nakasassu marayu dubu ashirin za su sami taimako wajen samun magani a cikin shekaru biyu masu zuwa.A cikin shirinmu na yau,za mu karanta muku wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya rubuto mana a kan wannan fanni.

Kusan a kowace shekara a wasu wuraren kasar Sin ana iya samun wasu jarirai marasa lafiya da iyayensu suka yar da su,hukumomin kula da marayu su kan tattara wadannan marayu suna renonsu.Duk da haka nakasassu marayu ba su iya yin kome yadda ya kamata ba,da ganin haka ma'aikatar kula da harkokin jama'a na gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin aiwatar da wani shirin taimakon nakasassu marayu,ta bai wa nakasassu marayu da shekarunsu ba su wuce 18 ba magani ko fida ta yadda za su iya samun koshin lafiya.

A ran biyu ga wata a nan birnin Beijing,Mista Li liguo,mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin ya bayyana cewa an samu sakamako a matakin farko wajen aiwatar da shirin nan cikin shekara fiye da daya da suka gabata.Ya ce "A cikin shekara daya,an yi wa nakasassu marayu fiye da 9100 fida,yawancinsu su sami iyalan da ake daukar rikonsu ta haka kuwa burinsu na sami iyalai masu koshin lafiya da kauna ya cika.

Lafiyar nakasassu marayu ta kara kyautatuwa bayan da aka yi musu fida.A da wasu marayu suna fama da ciwon zuciya,wasu kuwa lebunansu sun tsage.Bayan aka yi musu fida,yawancinsu sun warke.Wasu marayu dake fama da matsaloli na kwakwalwa ko na kafafuwa da hannaye,bayan da aka yi musu fida,sun sami sauki sosai.

Domin tabbatar da shirin taimakon nakasassu marayu tare da nasara,ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta tsara shirin aiwatar da shirin nan da kafa tsarin ka'idoji na kula da wannan shirin,ta kafa cikakken tsari da shirye-shiryen tafiyar da aiki.Gwamnatoci na wurare daban daban sun kuma shirya kungiyoyin ba da taimako da na kwararru likitoci.A sa'i daya kuma hukumomin kiwon lafiya na wurare daban daban sun ba da cikakken hadin kai ga kungiyoyin dake tabbatar da shirin nan a fannin fasaha.Mutane daga fannoni daban daban su ma ba da nasu taimako,kawo yanzu an sami kudin taimako na kudin Sin Renminbi Yuan miliyan 20 daga hukumomin gwamnati da maana'antu da kamfanoni da kuma kungiyoyin jama'a da mutane masu zaman kansu.

Mista Li Liguo,mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin ya ci gaba da cewa sun sami wasu matsaloli wajen tabbatar da shirin nan na taimakon nakasassu marayu,daya daga cikinsu shi ne ingancin asibitin da aka zaba a wasu wurare bai kai yadda ake bukata ba,a wasu wurare masu nesa an sami matsala wajen binciken lafiyar nakasassu marayu,aikin nan ya kasa samun cigaba yadda ya kamata a dukkan fannoni ba.Kan wadannan matsaloli,ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta dauki takamaiman matakai domin warware su a nan gaba kadan.Mista Li Liguo ya ce" Da farko kamata ya yi gwamnatoci na wurare daban daban su sake dudduba ingancin asibitocin da suka zaba domin daukar nauyin tabbatar da shirin nan ta yadda za a iya kammala aikin fida tare da nasara.Na biyu kuwa ofishin kula da aikin nan na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta Sin ya mai da hankalinsa wajen sa ido da bincike da kuma ba da jagora ga aikin nan.Na uku,a kara yawan asibiton dake tafiyar da shirin nan na taimakon nakasassu marayu da samar da sharuda nagarta ga nakasassu marayu,za su yi iyakacin kokarin warkar da su ta yadda za su iya samun koshin lafiya."Wannan jami'in ya ce gwamnatin kasar Sin ta zuba kudin Sin Renminbi Yuan miliyan dari shia a fannin nan.ta haka kuwa za a iyar warkad da nakasassu marayu kimanin dubu ashirin a cikin shekaru biyu masu zuwa.(Ali)