A ran 31 ga watan Oktoba, kungiyar ciniki ta duniya ta kira taro a birnin Geneva. Dayake yawancin kasashen da ke cikin kungiyar ba su gamsu da sabuwar shawarar da kawancen kasashen Turai ya gabatar a kan batun noma ba, shi ya sa an gama taron ba tare da samun sakamako ba. Saboda haka, kodayake daga yanzu zuwa lokacin kiran taron ministoci na kungiyar a Hongkong bai kai rabin wata ba, amma shawarwarin zagaye na Doha da kungiyar ciniki ta duniya ta shirya kan sha'anin noma bai sami mafita ba.
Ba da iznin shiga cikin kasuwanni babban batu ne da ke bukatar samun daidaituwa a gun shawarwarin da kungiyar take yi kan batun noma a wannan mataki . A farkon watan da ya shige, karo na farko ne wakilin ciniki na kasar Amurka Rob Portman ya gabatar da cewa, kasar Amurka tana son rage kashi 60 cikin dari na yawan taimakon da ta gabatar ga sha'anin noma na gidanta a cikin shekaru biyar masu zuwa, amma a sa'I daya, ya nemi kawancen kasashen Turai da kasar Japan da kowanensu ya rage kashi 80 cikin dari na yawan taimakon da suke gabatar wa sha'anin noma a gidajensu , sa'anan kuma ta nemi kawancen kasashen Turai da ya rage kashi 55 zuwa kashi 90 cikin dari na yawan kudadden fici da shigi na kwastan kan kayayyakin gona iri daban daban. Don amsar shawarar kasar Amurka, mamban kwamitin cinikayya na kawancen kasashen Turai Peter Mandelson ya bayyana cewa, kawancen kasashen Turai ya yarda da rage karin kudadden da zai samar wa ayyukan noma da yawancinsu zai kai kashi 70 cikin dari kawai, kuma a shirye ya ke zai rage kudaden shigi da fici na kwastan kan kayayyakin gona iri iri da kashi 20 zuwa kashi 50 cikin dari.
Wannan abin da kawancen nan ya gabatar ya gamu da kiyewa sosai daga yawancin mambobin kungiyar ciniki ta duniya. Bisa matsin da bangarori daban daban suka yi ne, A ran 28 ga watan jiya, Mr Mandelson ya bayyana cewa, kawancen kasashen Turai ya ke ya ci gaba da kokari wajen fannin ba da iznin shiga cikin kasuwanni, kuma ya yi shirin rage kudadden shigi da fici na kwastan na kayayyakin gona da yawansu zai kai kashi 35 zuwa kashi 60 cikin dari. Ya bayyana cewa, wannan ne matakin karshen na kawancen ya gabatar, bangaren kasar Amurka ya nuna rashin gamsuwa a kan wannan, ita kuma tana ganin cewa, abun da kawancen kasashen Turai ya yi bai isa abin da ake so ba.
Rukunin Cains da ke kunshe da kasashe 17 masu fitar da kayayyakin gona zuwa kasashen waje shi ma ya yi bakin ciki da sabuwar shawarar da kawancen kasashen Turai ya gabatar.Kasashe masu tasowa da yawa suna ganin cewa, kodayake sabuwar shawarar da kawancen kasashen Turai ya gabatar ta sami ci gaba bisa babban mataki, amma bai isa ba. Rukunin kasashe 20 sun taba wakiltar kasashe masu tasowa don neman Amurka da kasashen Turai da sauran kasashe masu ci gaba da su rage kudadden fici da shigi na kwastan kan kayayyakin gona da yawansu ya kai kashi 54 cikin dari, wasu kasashe masu fitar da auduga na Afrika su ma ba su gamsu da ci gaba da aka samu a halin yanzu wajen shawarwarin da ake yi kan batun noma ba. Suna ganin cewa, batun rage karin taimako da kasashe masu ci gaba suka samar wa noma bai jawo hankulan mutane sosai ba, kamar a ce an riga an gefantar da batun nan a wani gefe daban. Sun kuma yi kurarin cewa, idan ba za a iya daidaita batun auduga ba, to za su ki yin rangwamensu kan sauran battutuwan shawarwari da za a yi.
Bisa matsayin mambar kawancen kasashen Turai, kasar Faransa tana ganin cewa, sabuwar shawarar da Mr Mandelson ya gabatar ta wuce gona da iri. Ta kuma bayyana cewa, mai yiyuwa ne za ta musunta sakamakon karshe da za a samu a gun shawarwarin .
Sai rukunin kasashe goma da ke kunshe da kasar Japan da Switheland da Korea ta Kudu da Norway da sauran kasashen da ke shigar da kayayyakin gona sosai yana ganin cewa, rangwamen da kawancen kasashen Turai ya yi ya isa.
Bisa tsarin da aka tsai da, an ce, kasashe 148 da ke cikin kungiyar ciniki ta duniya suna bukatar daddale yarjejeniyar farko na shawarwarin sabon karo kan cinikin da ke tsakanin bangarori da yawa, wato shawarwarin zagaye na Doha, in ba haka ba ba za a kammala shawarwrin nan a karshen shekarar 2006 a gun taron ministoci da za a kira a Hongkong ba.(Halima)
|