Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 2 ga watan nan , Kungiyar addinin runkunin Maronite ta kasar Lebanon ta bayar da sanarwa , inda ta bayyana cewa yanzu bai kamata a tattauna matsalar yin murabus na shugaba Emile Lahoud ba .
Bayan da kungiyar ta yi taro a birnin Berut wannan rana ta bayar da sanarwa cewa , kudurin 1636 da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas kwanan baya mai hadari ne , kuma za ta kawo mugun tasiri ga halin da wannan shiyya ke ciki yanzu . Sanarwar ta yi gargadin cewa , tattauna matsalar yin murabus na shugaba Emile Lahoud zai sa kasar Lebanon ta shiga cikin halin hatsari , kuma zai lahanta tattalin arzikin kasar . Sanarwar ta yi kira ga bangarori daban daban da su girmama tsarin mulkin kasar kuma su kiyaye kwarjinin shugaban kasar . (Ado)
|