Mun sami labari daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, ran 1 ga wata fadar shugaban kasar Lebanon ta bayar da wata sanarwar cewa, Emile Lahoud, shugaban kasar yana fatan kudurin kwamitin sulhu na M.D.D. na 1636 zai kara saurin binciken al'amarin kashe Rafik Hariri, wato tsohon firayin ministan kasar.
Shugaba Lahoud ya bayyana imanin cewa, kwamitin binciken kasa da kasa da ke kula da al'amarin kashe Hariri zai ci gaba da samun goyon baya daga bangarori dabam daban, kuma yana fatan za a yi bincike a kan adalci, bincike wanda babu harkar siyasa a ciki, ta haka ne za a samu sakamakon da ake bukata. (Bilkisu)
|