Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-02 09:07:16    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(27/10-2/11)

cri
An fara wasannin kasashen Asiya ta Gabas na karo na 4 a Macao na kasar Sin daga ran 29 ga watan Oktoba zuwa ran 6 ga watan Nuwamba. Wasannin kasashen Gabashin Asiya da a kan yi sau daya a ko wadanne duk shekaru 4 kasaitaccen wasanni ne mafi girma a duk fadin Gabashin Asiya. A gun wannan wasanni, an kafa manyan gasanni guda 17, ciki har da guda 11 na wasannin Olympic; 'yan wasa fiye da dubu 3 daga kasashe da yankuna guda 9 ne suka shiga wannan wasanni. Kasar Sin ta kafa kungiyar wakilai mafi girma a tarihin wasannin kasashen Gabashin Asiya, 'yan wasanta 394 sun shiga manyan gasanni guda 16. Makasudin da ya sa kasar Sin ta shiga wannan wasanni shi ne neman samun maki mai kyau, da kuma horar da 'yan wasanta da za su iya gwada gwanintarsu a cikin wasannin Olympic na Beijing da za a yi a shekarar 2008.

Mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Jiang Xiaoyu ya bayyana a Macao a ran 29 ga watan Oktoba cewa, bikin bude wasannin kasashen Gabashin Aisya yana da kyau sosai, ya haskaka ra'ayoyin mutane kan bikin bude wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Yanzu kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing yana nan ne yana shiryawa bukukuwan bude da rufe wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008.

A daidai lokacin da ake yin wasannin kasashen Gabashin Asiya na karo na 4 a Macao na kasar Sin, hukumar birnin Beijing ta aiwatar da harkokin gabatarwa da al'adu a jere game da wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 a Macao. Wadannan harkoki sun hada da bikin dare na 'duniya daya, buri daya ga duk duniya' da bikin nune-nunen 'sabon Beijing, sabon wasannin Olympic' da taron ba da karin haske kan ayyukan shirya wasannin Olympic na Beijing da kuma bayar da kyautar litattafai kan ilmin Olympic ga 'yan makarantar mudil da na firamare na wurin.

Kwamitin gudanarwa na kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa ya ba da wata sanarwa a birnin Lausanne na kasar Switzerland a ran 27 ga watan Oktoba, inda ya tsai da kudurin yin kwaskwarima kan manyan gasanni guda 28 da za a yi a gun wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Abin da ya fi ba da tasiri kan kasar Sin shi ne kafa gasannin wasan kwallon tebur tsakanin kungiyoyin maza da kuma tsakanin kungiyoyin mata, a maimakon tsakanin maza biyu biyu da kuma tsakanin mata biyu biyu. Za a kuma kara yawan 'yan wasa mata a cikin wasannin Olympic. An kara yawan kungiyoyin wasan kwallon kafa da wasan kwallon Hockey da wasan kwallon ruwa wato water Polo na mata daga guda 10 zuwa guda 12. Sa'an nan kuma kwamitin wasan Olympic na duniya ya amince da kafa wasan gudu da ketare shinge mai tsawon mita dubu 3 na mata a cikin wasannin Olympic na Beijing, amma ya ki amincewa da kafa wasan dambe na mata, saboda haka wasan dambe da wasan kwallon gora sun zama manyan gasanni guda 2 ne kurum da babu 'yan wasa mata da za su shiga ciki a gun wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Tawagar Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Kasa da Kasa wato FIFA da ke kunshe da mutane 5 ta dudduba halin da kasar Sin take ciki wajen shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2007 a nan kasar Sin daga ran 27 ga watan Oktoba zuwa ran 4 ga watan Nuwamba. Za a yi wannan gasa a biranen Tianjin da Chengdu da Wuhan da Hangzhou da kuma Shanghai. Abubuwan da ke jawo hankalin kungiyar FIFA a wannan gami su ne filayen wasannin da ke wadannan birane 5 da kuma ko kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashe daban daban masu shiga gasar za su samu marhabin sosai a lokacin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata a shekarar 2007.(Tasallah)