Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-01 17:39:47    
Baki 'yan kasashen ketare na yin yawon shakatawa a kasar Sin cikin mota

cri

Akwai manyan hanyoyin mota biyu da baki 'yan kasashen ketare ke sha'awar binsu wajen yin yawon shakatawa a kasar Sin. Daya daga cikinsu ta tashi ne daga birnin Beijing zuwa birnin Shanghai, saura daya kuma ta hada birnin Beijing da birnin Xi'an. Da Malam Guo Wenbin, mataimakin babban manaja na babban kamfanin yawon shakatawa ta kasa da kasa ta Sin ya tabo magana a kan hanyoyin nan biyu, sai ya bayyana cewa, "dalilin da ya sa kamfaninmu ya tsai da wadannan manyan hanyoyin mota biyu da baki 'yan kasashen ketare ke binsu don yin yawon shakatawa a kasar Sin cikin mota, shi ne domin an sami ci gaba da sauri wajen shimfida tagwayen hanyoyin mota a kasar. Idan an tashi daga birnin Beijing zuwa birnin Shanghai cikin mota, za a shafe kwanaki 12 wajen yin ziyarar in an bi ta birnin Tianjin da shahararren dutse mai suna Taishan da birnin Qufu da birnin Xuzhou da birnin Suzhou, kuma ana yawon shakatawa a wadannan wurare masu ni'ima. Haka nan kuma wata babbar hanyar mota daban ita ce ke hada birnin Beijing da birnin Xi'an. In an shiga mota daga birnin Beijing zuwa birnin Xi'an, tafiyar za ta kai ta kwanaki 9. A lokacin tafiyar nan, za a sami damar yin yawon shakatawa a birnin Baoding da birnin Anyang da birnin Zhenzhou da birnin Luoyang da Sanmenxia da dai sauran shahararrun wuraren yawon shakatawa."

Malam Guo ya kara da cewa, yanzu, gine-gine da ake saukar da masu yawon shakatawa da kuma wuraren yawon shakatawa kullum sai kara kyautatuwa suke yi a wadannan birane da ke a bakin wadannan manyan hanyoyin mota biyu. Idan wani dan yawon shakatawa ya shafe kwana 1 ko biyu yana yawon shakatawa a ko wane birni, to, zai ji dadi sosai.

Malama Gao Feifei wadda ta shafe shekaru biyu tana aikin jagoranci ga wadanda ke yawon shakatawa tsakanin birnin Beijing da birnin Shanghai cikin mota, ta bayyana cewa, "masu yawon shakatawa sun fi sha'awar kallon gine-gine da al'adu irin na gargajiya. Alal misali, a birnin Beijing, su kan ziyarci fadar sarkunan kasar Sin da babbar ganuwa da sauransu, a birnin Qufu, su kan ziyarci haikalin Confucius da makamantansa. A birnin Xuzhou kuma su kan ziyarci tsoffin kaburbura na zamanin daular Han da dai sauransu. Ban da wannan kuma birnin Shanghai babban birnin kasa da kasa ne iri na zamani, a nan ne masu yawon shakatawa za su iya yin sayayya, su dandana abinci masu dadin ci iri daban daban."

Malama Gao ta ci gaba da cewa, yayin da baki masu yawon shakatawa ke tafiya cikin mota, su kan ga abubuwan da suke sha'awa ainun a bakin hanyoyin mota, a cikin irin wannan hali ne, sai su kan nemi direba da ya tsayar da mota, su sauka daga mota, su kara more idonsu da abubuwan nan, kuma su kan dauki hotuna.

Yanzu, baki da yawa da suka fito daga Amurka da Turai da kuma sauran kasashe suna sha'awar yin yawon shakatawa ainun a kasar Sin cikin mota. Malam Bill Milewski, dan kasar Amurka ya taba yin irin wannan yawon shakatawa har sau uku. Ya ce, "don mu baki 'yan kasashen ketare, lokacinmu na yin yawon shakatawa a kasar Sin bai yi yawa ba. Sabo da haka ba mu son daukar jirgin sama daga birnin Beijing zuwa birnin Shanghai kai tsaye ba. Idan na tashi daga birnin Beijing zuwa birnin Shanghai cikin mota, to, zan iya samun damar yin yawon shakatawa a dutsen Taishan da haikalin Confucius da kuma sauran wurare masu ni'ima. Yayin da muke tafiya cikin mota, zan iya kallon al'adun gargajiya na kasar Sin da kuma sabbin abubuwa da ke faruwa a kasar."

Malam Zhang Shuo, daya ne daga cikin manajojin babban kamfanin yawon shakatawar kasa da kasa na Sin ya ce, ban da hanyar nan, kuma baki 'yan kasashen waje su kan dauki mota wajen yin yawon shakatawa daga birnin Beijing zuwa birnin Xi'an cikin mota. A birnin Xi'an za a ga tsoffin kayayyaki masu dimbin yawa da aka tono daga karkashin kasa. Ya kuma yi maraba da masu yawon shakatawa na kasashen ketare da su yi yawon shakatawa a kasar Sin cikin mota. (Halilu)