Kwanan baya, jami'ai fiye da 20 wadanda ke kula da ayyukan kiyaye muhalli na kasashe 19 na Afirka sun zo nan birnin Beijing don halartar kwas din yin horo da babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ta shirya. Mr. Hong Shaoxian, jami'in wannan babbar hukuma wanda ke kula da aikin yin hoto ya bayyana cewa, kwas din yin horo ya gabatar da wani muhimmin dandali ga jami'an kiyaye muhalli na kasashen Afirka domin koyon fasahohin kiyayye muhalli na kasar Sin, wannan zai sa kaimi ga yin mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wajen kiyaye muhalli. To, jama'a masu sauraro yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya rubuto mana kan wannan labari.
Babban yankin Afirka wata nahiya ce wadda take da kasashe masu tatowa mafiya yawa. A lokacin da wadannan kasashe suke bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasashensu, kuma sun yi kamar yadda kasar Sin take wato suna fuskantar matsalar kiyaye muhalli. Domin kara yin hadin gwiwa da musanye-musanyen fasahohin da aka samu wajen kiyaye muhalli, a watan Fabrairu na wannan shekara a birnin Neirobi, hedkwatar kasar Kenya, an yi taron kiyaye muhalli na kasar Sin da kasashen Afirka. A gun taron, Zeng Peiyan, mataimakin firayim ministan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara hadin gwawa da yin mu'amala a tsakaninta da kasashen Afirka wajen kiyaye muhalli, kuma tana son taimaka wa kasashen Afirka don horad da kwararrun mutane masu kiyaye muhalli, da bayyana wa kasashen Afirka fasahohin da ta samu daga wannan fanni.
Afirka tana karancin albarkatun ruwa sosai, kuma barbazuwar albarkatun ruwa ba ta kasance bai daya ba, kuma an kazamtar da ruwa sosai. Domin daidaita wannan matsala, a watan Satumba na wannan shekara, babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ta kafa kwas din yin horo dangane da matsalolin kazancewar ruwa da aikin kula da albarkatun ruwa, an ilmantar da jami'ai masu kiyaye muhalli na kasashen Afirka domin daidaita wadannan matsaloli. Mr. Hong Shaoxian, jami'in wannan babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin wanda kuma ke kula da aikin yin hoto ya bayyana cewa, "Kasar Sin ta taba gamuwa da tarin wahaloli a fannin kiyaye muhalli, musamman ma ga matsalar yin rigakafin kazancewar ruwa, da yin amfani da albarkatun ruwa, kuma ta samu fasahohi masu kyau daga wadannan fannoni. Ba'idin haka kuma ya kasance da kamanci sosai a wasu fannoni a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wato dukkansu suna da hamada da wurare masu fama da bala'in fari, fasahohin da kasar Sin ta samu suna da amfani kwarai ga kasashen Afirka domin daidaita wadannan matsaloli."
An ce, ta hanyar koyo da yin ziyara a wasu wuraren kasar Sin, jami'an kiyaye muhalli na kasashen Afirka ba ma kawai sun samu ilmin kiyaye muhalli da fasahohin aikinsu daga wajen kasar Sin ba, hatta ma sun fahimci fasahar kiyaye muhalli na kasar Sin sosai. Mr. Hong ya ce, bayan rufe kwas din yin horo, jami'an kiyaye muhalli na kasashen Afirka sun nuna yabo sosai ga wannan aikin yin horo. "Jami'ai masu halartar kwas din yin horo suna fatan kasashensu za su iya kara aikawa da mutane da yawa zuwa kasar Sin don yin koyo da kuma yin ziyara, ba ma kawai za su yi koyi da kasar Sin wajen hasashe ba, a'a abu mafi muhimmanci shi ne za su fahimci yadda kasar Sin take tafiyar da ayyukanta wajen kiyaye muhalli a yayin da take bunkasa tattalin arzikin kasar da sauri kamar haka, sun bayyana cewa, fasahohin kasar Sin suna da babbar ma'ana ga bunkasa kasashensu". (Umaru)
|