Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-26 16:22:10    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(20/10-26/10)

cri
An rufe wasannin duk kasar Sin na karo na 10 a birnin Nanjing na gabashin kasar Sin a ran 23 ga wannan wata. Wasannin duk kasar Sin da a kan yi sau daya a ko wadanne shekaru 4 wasanni ne na matsayin koli da a kan shirya a duk fadin kasar Sin. 'Yan wasa kimanin dubu 10 sun shiga wannan wasannin da aka bude a ran 12 ga watan nan. A cikin kwanaki 12, 'yan wasan kasar Sin sun karya matsayin bajimta na duniya a cikin wasanni guda 6, ciki har da wasan daukan nauyi da harbe-harbe, haka kuma wasu 'yan wasa matasa sun gwada gwanintarsu. An mayar da wadannan wasanni a matsayin rawar daji ga wasannin Olympic na Beijing da za a yi a shekarar 2008 daga duk fannoni, an sami fasahohi na shiryawa daga wannan wasanni, an kuma horar da 'yan wasan kasar Sin da za su iya gwada gwanintarsu a cikin wasannin Olympic na Beijing.

Lokacin da yake halartar bikin baje-koli na kasar Sin da Kawancen Kasashen Kudu maso Gabashin Asiya da aka bude a birnin Nanning na kudancin kasar Sin a ran 19 ga wata, mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Jiang Xiaoyu ya bayyana cewa, yanzu kudin da aka tattara don wasannin Olympic na Beijing ya riga ya zarce kudin da ake neman samu a lokacin neman samun damar shirya wasannin Olympic na Beijing, wannan ya dasa wani ingantaccen tushe ne a fannin kudi wajen gudanar da wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 lami lafiya. Kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing zai tabbatar da makasudin samun ribar da yawanta ya kai dalar Amurka miliyan 16.

An yi bikin gina filin wasannin Jami'ar Kimiyya ta Beijing a ran 18 ga wata, inda za a yi gasannin wasan judo da karate a lokacin wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Daga nan ne, an fara gina dukan sababbin filayen wasanni guda 11 don wasannin Olympic a nan Beijing. Ana bukatar filayen wasanni guda 37 don wasannin Olympic na shekarar 2008, ciki har da guda 31 a nan Beijing, wasu 6 a Qingdao da Shanghai da Tianjin da Shenyang da Qinhuangdao da kuma yankin musamman na Hong Kong. A cikin filayen wasanni guda 31 da ke nan Beijing, za a gina sabbabin filayen wasanni guda 11, za a kyautata wasu 11, za a gina wasu 9 a matsayin filayen wasanni na rikon kwarya.

Hukumar birnin Beijing ta ba da wata sanarwa a ran 21 ga wata cewa, saboda za a yi wasannin kasashen Asiya ta Gabas na karo na 4 a Macao na kasar Sin daga ran 29 ga watan Oktoba zuwa ran 6 ga watan Nuwamba, shi ya sa Beijing za ta tafiyar da harkokin gabatarwa da na al'adu da suka shafi wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 a Macao daga ran 25 ga watan nan zuwa ran 6 ga watan Nuwamba.

Bisa wani binciken da aka bayar a Hong Kong a ran 22 ga wata, an ce, yawancin mazaunan Hong Kong suna goyon bayan Hong Kong da ta ba da taimako ga Beijing wajen yin gasannin fasahar hawan doki na wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Binciken da aka yi ya nuna cewa, mutanen da aka yi musu tambayoyi da yawansu ya kai kashi 64 bisa dari suna ganin cewa, ba da taimako ga Beijing wajen yin gasannin fasahar hawan doki yana iya daga matsayin Hong Kong a duniya, ya kuma ba da taimako wajen ingiza bunkasuwar aikin yawon shakatawa na Hong Kong.(Tasallah)