Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-26 16:06:05    
Cikin gaggarumin hali ne kasar Sin ta yi harkar tunawa da ranar cika shekaru 60 da aka sake karbar Taiwan

cri

Yau ran 25 ga watan nan rana ce ta cika shekaru 60 da Taiwan, muhimmin tsibirin da ke a kudu maso gabashin kasar Sin ta raba kanta daga mulkin mallaka na Japan kuma ta dawo cikin kasar mahaifa. Yau da safe mutane na da'irori daban daban na kasar Sin sun yi ayyuka cikin gaggarumin hali a nan birnin Beijing, a gun wannan babban taro Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ya yi jawabi, inda ya nuna cewa, dawowar Taiwan a kasar mahaifa sakamako ne na babbar nasarar da jama'ar kasar Sin suka samu a cikin yakin kare harin Japan, nasara da alfahari ne ga duk al'ummar kasar Sin. Muna yin harkar tunawa da sake dawowar Taiwan a kasar mahaifa ne don tunawa da tarihi, kada a manta da zamanin da, a kiyaye mallakar kai da cikakken yankin kasa don sa kaimi ga aikin hada kasar mahaifa cikin lumana. Yanzu sai ku saurari labarin da aka ruwaito mana.

A shekara ta 1894 kasar Japan ta ta da yakin kawo wa kasar Sin hari, kuma ta tilasta wa gwamnatin sarautar Qing ta sa hannu kan yarjejeniyar rashin adalci, kuma ta mamaye Taiwan.

Shekaru 60 ke nan wato a ran 25 ga watan Oktoba na shekara ta 1945, wato lokacin da jama'ar kasar Sin ta yako nasara kan maharan Japan, gwamnatin kasar Sin ta sake karbar Taiwan.

A gun babban taron tunawa da ranar cika shekaru 60 da aka sake karbar Taiwan, Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya nuna cewa, Dawowar Taiwan a kasar mahaifa sakamako ne na babbar nasarar da jama'ar kasar Sin suka samu a cikin yakin kare harin Japan, nasara da alfahari ne ga duk al'ummar kasar Sin. Muna yin harkar tunawa da sake dawowar Taiwan a kasar mahaifa ne don tunawa da tarihi, kada a manta da zamanin da, a kiyaye mallakar kai da cikakken yankin kasa, mu yada babban ruhu na al'ummar kasar Sin, mu himmantar da 'yanuwa na gabobi biyu da su hada kai su kiyaye mallakar kai da cikakken yankin kasa don sa kaimi ga aikin hada kasar mahaifa cikin lumana.

A cikin rabin karnin da 'yanuwa na Taiwan suka yi gwagwarmaya da maharan Japan, yawan mutanen Taiwan da suka sadaukar da ransu ya kai dubu 650, sun yi amfani da jini da rai don shaida cewa, su Sinawa ne. A gun babban taron da aka yi yau, Mr. Zhou Qing wanda ya ganam ma idonsa da dawowar Taiwan a kasar mahaifa ya nuna cewa, Lallai ba mu sake karbar Taiwan a sanga ba, ya kamata mu kara darajanta zaman lafiyar duniya. Ya kamata mu hana wai 'yancin kan Taiwan da tsirarrun mutanen da ke neman jawo wa kasar mahaifa baraka su ke yi, mu sa kaimi ga yalwatuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu don hada kasar mahaifa cikin lumana, kuma mu zabga fama domin sake tasowar al'ummar kasar Sin. (Dogonyaro)