Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-24 16:10:55    
Ziyarar sakataren tsaron kasar Amurka a Sin ta inganta ma'amala da hadin kai a tsakanin askarawan kasashen biyu

cri
Bayan da sakataren tsaron kasar Amurka Donald Henry Rumsfeld ya gama ziyarar aiki ta aminci da ya shafe kwanaki biyu yana yinta a kasar Sin a ran 20 ga wata, sai ya tashi daga nan birnin Beijing. Bayan haka yayin da maneman labarun kasar Sin suka kai ziyara ga Malam Zhang Bangdong, shugaban ofishin kula da harkokin waje na ma'aikatar tsaron kasar Sin don jin ta bakinsa, sai ya bayyana cewa, ziyarar Rumsfeld ya kara kawo fahimtar juna a tsakanin rundunonin sojojin kasar Sin da na Amurka, kuma ta inganta ma'amala da hadin kai a tsakanin bangarorin nan biyu, sabo da haka ziyarar tana da matukar muhimmanci ga yalwata hulda da ke tsakanin rundunonin sojojin kasashen biyu da kuma tsakanin kasashen biyu.

A lokacin ziyararsa, Rumsfeld ya yi ganawa da tattaunawa tsakaninsa da shugabannin kasar Sin da na rundunar sojojin kasar, kuma ya ziyarci hedkwatar sojojin madafu ta biyu ta kasar Sin da Jami'ar Koyon Aikin Soja ta kasar. Dangane da ziyararsa, Malam Zhang Bangdong ya bayyana cewa, "a lokacin da Rumsfeld ke yin ziyara a kasar Sin, shugabannin kasarmu sun bayyana masa burin kasar Sin na kara yalwata huldar aminci da hadin kai a tsakanin rundunar sojojin kasashen nan biyu, sun bayyana muhimmancin huldar da ke tsakanin kasashen biyu da rundunar sojojinsu, sa'an nan bangaren kasar Sin ya bayyana masa matsayin ka'idarmu a kan matsalar Taiwan, da manufofin kasar Sin game da tsaron kasa, da kuma matsayin ka'idojin kasar Sin a kan kare zaman alfiyar duniya da yaki da ta'addanci da yin adawa da darikar gwagwarmayar siyasa da dai sauransu.

Matsalar Taiwan babbar matsala ce mai matukar muhimmanci ga huldar da ke tsakanin Sin da Amurka wadda ke jawo hankulan mutane sosai, sabo da haka matsalar nan wata babbar matsala ce da aka yi tattaunawa a kai a lokacin ziyarar da Rumsfeld ke yi a kasar Sin. Malam Zhang Bangdong ya ci gaba da cewa, "shugabannin kasar Sin sun bayyana wa kasar Amurka a kan yadda suke lura da matsalar Taiwan sosai, sun bukaci kasar Amurka da kada ta nuna alamar kuskure ga 'yan a-ware na Taiwan, kuma kada ta sayar wa Taiwan da makamai, kada ta inganta ma'amalar aikin soja a tsakaninta da Taiwan. Wannan yana da matukar muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan. Kullum kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a kan wannan matsayin ka'ida."

Malam Zhang Bangdong ya ce, Rumsfeld ya sha nanata matsayin ka'ida da kasar Amurka ke tsayawa a kai dangane da matsalar Taiwan a wurare daban daban, tun ba yau tun ba jiya ba, gwamnatin Bush tana tsayawa kan matsayinta dangane da matsalar Taiwan, maganar Bush kuma ba ta tashi, wato kasar Amurka tana nacewa ga bin sanarwoyi guda uku da aka bayar cikin hadin guiwa tsakanin Sin da Amurka. Amma Malam Zhang Bangdong yana ganin cewa, wajibi ne, a kara yin tattaunawa kan matsalar Taiwan tsakanin Sin da Amurka, ta yadda matsalar nan ba za ta zama tarnaki ga yalwatuwar hulda tsakanin rundunar sojojin kasashen biyu ba. Ya ce, yana sa ran alheri ga abubuwa da za su wakana nan gaba dangane da yalwatuwar huldar da ke tsakanin rundunar sojojin kasashen biyu, kan hakan sai Malam Zhang Bangdong ya bayyana cewa, "kamata ya yi, a ce, huldar da ke tsakanin rundunonin sojojin kasar Sin da na Amurka tana da matukar muhimmanci ga huldar da ke tsakanin kasashen biyu, Ya kamata, bangarorin biyu su kara yin ma'amala a tsakaninsu da kara karfin hadin guiwarsu. Tun da yake huldar da ke tsakanin Sin da Amurka na kara samun yalwatuwa taki kan taki, mun amince cewa, huldar da ke tsakanin rundunonin sojojin kasashen biyu ma za ta kara samun yalwatuwa a nan gaba." (Halilu)