Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-21 19:29:04    
Kasar Sin da kasar Amurka sun yi shawarwari a kan hadin guiwar da ke tsakaninsu da sojojinsu

cri

A ran 19 ga wannan wata a nan birnin Beijing, ministan tsaron kasa na kasar Amurka Donald Henry Rumsfeld wanda ke yin ziyarar aiki ta sada zumunta yanzu a kasar Sin ya soma manyan ayyukan da zai yi a gun ziyarar nan a kasar Sin, bi da bi ne ya gana da manyan shugabannin kasa da na soja na kasar Sin don yin shawarwari a kan babban shirin yin hadin guiwar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu . Gaba daya ne bangarorin biyu suka bayyana cewa, suna son ci gaba da inganta ma'amala da hadin guiwa da ke tsakanin sojojin kasashen biyu da kuma sa kaimi ga samun sabon ci gaba wajen huldar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu.

Ziyarar da Mr Rumsfeld yake yi a nan kasar Sin ta zama karo na farko da yake  yin ziyara a kasar Sin tun bayan da ya hau mukaminsa na sakataren  tsaron kasa na kasar Amurka tun daga shekarar 2001. Shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya Hu Jintao da mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya kuma ministan tsaron  kasar Sin Cao Gangchuan da sauran manyan shugabannin kasa da na soja na kasar Sin bi da bi ne suka gana da shi, kuma sun yi shawarwari masu zurfi a kan battutuwan da suka jawo hankulan kasashen biyu da sojojinsu cikin  sakin jiki, Mr Hu Jintao ya nuna yabo mai yakini ga ziyarar da Mr Rumsfeld yake yi a nan kasar Sin. Ya bayyana cewa, dukkan ayyukan da ake yi a gun ziyarar suna da amfanin kara wa sojojin kasashen biyu fahinta da zumunci, tabbas ne za su ba da babban taimakon sa kaimi ga raya huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shawararin da ke tsakanin ministocin tsaron kasa na kasashen biyu ya jawo hankulan mutane sosai da sosai. Abubuwan da aka yi shawarwari a kansu sun jibinci huldar da ke tsakanin shiyya shiyya da halin da ake ciki tsakanin kasa da kasa da makomar raya huldar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu da sauran fannoni. Mr Rumsfeld ya bayyana cewa, ziyarar nan ta kara masa fahimtar sojojin kasar Sin, ya bayyana cewa, ta hanyar ziyarar nan, na gane cewa, tamkar yadda muke tsammanin yin wani al'amari a cikin ma'aikatar tsaron kasa ta Amurka, minista Cao Gangchuan da sojojinsa suna son kara yin ma'amala ta hanyoyi daban daban don aiwatar da wasu ayyuka ta yadda za a iya kawar da rashin fahimta a tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu, kasar Sin tana nan tana yin ayyukan zamanintar da sha'anin soja, Mr Cao Gangchuan ya gabatar da shirin kasar Sin wajen yin hadin guiwa a nan gaba a tsakanin sojojin kasashen biyu wato Sin da Amurka. Ya bayyana cewa, kafa huldar da ke tsakanin sojojin kasashen biyu bisa tushen yin bincike da hadin guiwa da samar da sakamako ya dace da moriyar juna na bangarorin biyu . Kullum muna mayar da huldar da ke tsakanin sojojin kasashen biyu bisa matsayin muhimmin kashi da ke cikin huldar da ke tsakanin kasashen biyu .

Lokacin da ya tabo magana a kan batun Taiwan da ya jawo hankulan mutane sosai, a gun shawarwarin da ya yi a jeri, Mr Rumsfeld ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Amurka tana tsayawa tsayin daka ga aiwatar da manufar Sin daya tak a duniya, kuma tun daga farko har zuwa karshe, tana tsayawa kan matsayinta na aiwatar da hadaddiyar sanarwa guda uku da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Bangaren kasar Sin shi ma ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana son daidaita batuttuwan da ke jawo hankulan mutane a cikin huldar da ke tsakanin kasashen biyu bisa ra'ayi mai yakini don kafa ingantaccen tushen raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka.(Halima)