
A ran 20 ga wata a birnin Shanghai,Chen Liangyu,mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma sakatare na kwamitin jam'iyyar nan a birnin Shanghai ya gana da Mista Lien Chan,shugaban jam'iyyar Kuomintang da aka girmama sunansa da 'yan rakiyarsa.
A lokacin ganawar,Chen Liangyu ya sanar da Lien Chan kan cigaban da aka samu a fannoni uku wajen bunkasa dangantaka ta tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan,wato na farko a tabbatar da ra'ayoyi bai daya da sakatare-janar Hu Jintao da shugaba Lien Chan suka samu,na biyu a kago yanayi mafi kyau ga 'yanuwan Taiwan wajen zamansu da aikinsu da kuma zuba jari da shigar 'ya'yansu a makarantu.Na uku a yi iyakacin kokarin bayar da taimako wajen kara bunkasa dangantaka ta tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan.(Ali)
|