A watan Yuni na shekarar da muke ciki, a gun taron ministocin kudi na kungiyar kasashe 8 an shelanta cewa, za su rage da soke basusuka dalar Amurka wajen biliyan 40 da kasashe mafiya talauci 18 suka ci. Kasashe 14 daga cikin wadannan kasashe 18 suna kudu da Sahara. Amma sharudan siyasa da na tattalin arziki na rage da soke wadannan basusuka sun sa kasashen Afirka da su gane cewa, wannan ba waina ce da ta zo daga sama ba.
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasashen yammacin duniya suna ganin cewa, kasashen Afirka suna da wadatattun albarkatun halitta iri iri da babban boyayyen kasuwa. A sa'i daya, a bakin yaki da ta'addanci, kasashen yammacin duniya sun fara sake duba manufofinsu na Afirka, sun kuma sa kaimi ga kamfanoninsu da su kara zuba jari a Afirka kuma da su kara yin mu'amala kan harkokin siyasa da tattalin arziki da tattalin arziki da cinikayya da harkokin soja da kasashen Afirka.
Ban da shirin rage da soke basusukan da aka ci, a gun taron shugabannin kungiyar kasashe 8 da aka yi a watan Yuli na shekarar da muke ciki, wadannan kasashe 8 na yammacin duniya sun yi shelar kara yawan taimakon kudin dalar Amurka kimanin biliyan 50 da za su samar wa kasashen Afirka.
Amma yanzu ana ganin cewa, a fili ne hanyoyin yin mu'amala da kasashen yammacin duniya ciki har da kasar Amurka da kasar Ingila da kasar Faransa suke bi suna dacewa da bukatun da suke nema kuma da moriyarsu kwarai. Lokacin da kasashen yammacin duniya suka yi shelar rage da soke basussukan da kasashe mafiya talauci suka ci, sun neme su da su kara bude kasuwanninsu da aiwatar da manufofin yin ciniki cikin 'yanci. Amma yanzu kasashen Afirka suna ganin cewa, yin ciniki cikin 'yanci da kasashen yammacin duniya masu hannu da shuni suke nema yana daya daga cikin dalilan da ke bata bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka.
Yanzu, kasashe masu tasowa, musamman kasashe mafiya fama da talauci ba su iya yin cinikin waje da kasashe masu ci gaba cikin halin daidai wa daida ba. Lokacin da kasashe masu ci gaba suke neman yin ciniki cikin 'yanci da kakkausar harshe, suna ba da kudin rangwame masu dimbin yawa kan kayayyakinsu. Suna kuma sa katangar harajin kwastam da irin wadda ba ta harajin kwastam ba ga kayayyakin da aka shigo da su daga kasashe masu tasowa. Alal misali, kasashen yammacin duniya suna ba da kudin rangwame sosai kan amfanin gona, wannan ya sa amfanin gona na kasashen Afirka ba su da karfin yin gasa da amfanin gona na kasashe masu ci gaba. Amma kowa ya sani, amfanin gona muhimman kayayyaki ne da kasashen Afirka suke fitarwa. Sabo da haka, idan kasashen Afirka sun kara bude kasuwanninsu kwata kwata, shi ke nan, hasarar da kasashe masu ci gaba suka ci domin rage basusukan da suka yi ba za ta iya samun ramuwar diyya ta hanya daban ba.
Haka nan kuma, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasashen Amurka da Ingila sun sa yankunan Afirka da su zama muhimman wuraren yin yaki da ta'addanci. Bayan aukuwar matsalar Ran 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2001, a ganin kasashen yammacin duniya, asalin fitowar ta'addanci shi ne talaucin da ya faru a kasashe maras samun ci gaba, wannan ya sa jama'arsu da su yi adawa da kasashe masu ci gaba. A hankali a hankali tunaninsu ya zama ta'addanci. Sabo da haka kasashen yammacin duniya sun damu, idan ba a kula da halin fama da talauci da kasashen Afirka suke ciki ba, mai yiyuwa ne wadannan kasashe su zama wuraren da ke haifar da ta'addanci. A sakamakon haka, babu sauran hanyar da za su iya zaba, sai su fara mai da hankulansu kan halin fama da talauci da kasashen Afirka ke ciki domin zaman karko nasu.
Bugu da kari kuma, aiwatar da kyawawan manufofin siyasa da kafa gwamnatin da za ta iya aiwatar da manufofinta a fili kuma da yin yaki da almubazzaranci da rashawa su ma sharuda ne na rage da soke basusukan da kasashe masu ci gaba suka kafa. Ko shakka babu wadannan sharuda sun zama damar sa hannu a cikin harkokin gida na kasashen Afirka da kasashe masu ci gaba za su yi amfani da su. Yanzu wasu 'yan siyasa na kasashen Afirka masu nuna juyayi sun gane ainihin burin da kasashe masu ci gaba ke nema. Sun bayyana cewa, soke katangar cinikin waje da kasashe masu ci gaba suka sa kuma da kafa sabuwar odar tattalin arzikin duniya su ne aihinin hanyar kawar da talauci daga Afirka. (Sanusi Chen)
|