Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-19 07:55:49    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(13/10-19/10)

cri
An bude wasannin duk kasar Sin na karo na 10 a birnin Nanjing da ke gabashin kasar Sin a ran 12 ga wata, wasannin nan da a kan shirya sau daya a ko wadanne shekaru 4 kasaitaccen wasanni ne mafi girma da kasar Sin ta shirya. An kafa manyan wasanni 32 a cikin wannan gami, ciki har da dukan manyan wasanni na wasan Olympic, 'yan wasa kimanin dubu 10 daga larduna da jihohi masu tafiyar da harkokinsu da kansu da biranen da ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye na babban yankin kasar guda 31 da kuma yankunan musamman na Hong Kong da Macao sun shiga wannan wasanni, yawan 'yan wasa da na wasanni ya karya matsayin bajimta a tarihin dukan wasannin duk kasar Sin. Za a kammala dukan gasanni a ran 23 ga watan nan.

Lokacin da yake halartar wasannin duk kasar Sin na karo na 10 a birnin Nanjin a ran 12 ga wata, shugaban Kwamitin Wasan Olympic na Kasa da Kasa Jacques Rogge ya yaba wa kasar Sin saboda bunkasuwar da ta samu a fannin wasan motsa jiki. Mr. Roggeya ce, wasannin duk kasar Sin wani muhimmin aiki ne ga kasar Sin, saboda babban karfin da kasar Sin ta nuna wajen wasan motsa jiki, shi ya sa gasannin neman shiga karon karshe na wasannin duk kasar Sin sun fi na share fage domin wasan Olympic tsanani. 'Yan wasan kasar Sin sun nuna babban karfinsu a wasannin Olympic na Athens, kungiyar wakilan kasar Sin za ta sake samun babbar nasara a cikin wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing a shekara ta 2008, bayan wannan wasannin duk kasar Sin.

A cikin karon karshe na gasar iyon rigingine mai tsawon mita 100 ta maza ta wasannin duk kasar Sin na karo na 10 da aka yi a birnin Nanjing da ke gabashin kasar a ran 15 ga wata, dan wasan lardin Jiangxi Ouyang Kunpeng ya karya matsayin bajimta na Asiya da dakikokin 54 da 09.

Mataimakin babban darektan Hukumar Yaki da Magani Mai Sa Kuzari ta Duniya Mr. Rune Andersen ya darajanta kasar Sin a ran 16 ga wata saboda aikin yakin da magani mai sa kuzari da kasar Sin ta yi a cikin wasannin duk kasar Sin na karo na 10. Mr. Andersen ya dubbuba aikin yaki da magani mai sa kuzari na wasannin duk kasar Sin na karo na 10 a kwanan baya, ya bayyana cewa, hanyar binciken magani mai sa kuzari da aka bi a wannan gami ta dace da bukatar Hukumar Yaki da Magani Mai Sa Kuzari ta Duniya daga duk fannoni, an gwada gwaninta sosai a wannan fanni.

Jami'in kula da lafiyar al'umma na wasannin Olympin na Beijing na shekarar 2008 kuma mataimakin darekatan Cibiyar Sarrafa Ciwace-ciwace ta Beijing Gao Xing ya bayyana a ran 15 ga watan nan cewa, za a bayar da halin da ake ciki wajen yaduwar annobar a ko wace rana a gun wasannin Olympic da za a yi a nan birnin Beijing a shekara ta 2008, don tabbatar da lafiyar al'umma. Mr. Gao Xing ya yi wannan bayani ne a gun dandalin tattaunawar likitancin ceto na duniya na karo na 3 da aka yi a birnin Guilin da ke kudancin kasar Sin.

An yi gasar gudun dogon zango wato Marathon ta duniya ta shekarar 2005 a nan birnin Beijing a ran 16 ga wata. 'Yar wasan kasar Sin Sun Yingjie ta zama zakara a cikin kungiyar mata, dan wasan kasar Kenya Benson Cherono ya zama zakara a cikin kungiyar maza. 'Yan wasa daga kasashe da yankunan duniya fiye da 30 sun shiga wannan gasa.(Tasallah)