Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-13 17:35:08    
Babbar Panda alama ce ta zaman lafiya da kauna

cri

Babbar Panda wadda jama'a ke ba ta sunan "abu mai daraja na kasar Sin" don nuna mata girmamawa, wadda kuma ke da makaunacciyar fuska, fatarta da gashinta suna da taushi, takan yi wasanni masu ban sha'awa, kuma ta yi kamar mutun wajen cin abinci, sabo da haka ta zama daya daga cikin dabbobin da suke fi ba wa mutane sha'awa da kauna na duniya. A lokacin da aka kafa asusun dabbobin daji na duniya a shekarar 1961, an dauki hoton babbar Panda da ya zama hoton da ke kan tuta da kuma tambarin kungiyar.

Tun a shekarar 685, sarkin daular Tang ya ba wa sarkin kasar Japan na wancan zamani kyautar manyan Panda guda 2. Wannan ya zama karo na farko ke nan da manyan Panda na kasar Sin sun fita daga kasar Sin bisa matsayinsa na "manzon sada zumunci".

A shekarar 1870, an nuna wani samfurin babban Panda a babban dakin ajiye kayayyakin halittu na Paris, wannan ya girgiza duk duniya baki daya.

Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, ta ba wa tsohuwar Tarayyar Soviet kyautar babbar Panda ta farko a shekarar 1955, bayan shekaru 2 kuma an aika da wata babbar Panda daban zuwa birnin Moscow, wadannan Pada guda 2 sun zama dabbobin da mutanen Moscow suka fi nuna kauna a wancan lokaci.

A lokacin da Nixon, tsohon shugaban Amurka ya kawo ziyarar a kasar Sin a shekarar 1972, gwamnatin kasar Sin ta ba wa jama'ar Amurka kyautar manyan Panda guda 2 masu suna "Lingling" da "Xingxing". A lokacin da wadannan Panda guda 2 suka isa Amurka, ko da yake ana ruwa amma mutane har 8000 na kasar sun tarye wadannan "manzanin aminci" guda 2 da suka zo daga kasar Sin.

Cikin shekaru 28 da suka wuce wato daga shekarar 1955 zuwa ta 1982, bi da bi ne kasar Sin ta ba da kyautar manyan Panda har 24 ga kasashe 9 wato tsohuwar Tarayyar Soviet da Korea ta Arewa da Amurka da Japan da Faransa da Ingila da Mexico da Spain da Tarayyar Jamus. Manyan Panda sun riga sun zama "manzanin sada zumunci da zaman lafiya" da ke alamanta kaunar jama'ar Sin.

A kwanan a tashi, wasu manyan Panda daga cikin wadannan "manzanin kasar Sin" sun riga sun mutu, zuwa shekarar 2002, sai Panda 15 kawai suke da rai a duniya.

Bayan shekarar 1985, gwamnatin kasar Sin ba ta taba bai wa kasashen waje kyautar manyan Panda ba. Amma kasashe da yawa sun gayyaci manyan Panda na kasar Sin da su kai "ziyara" a kasashensu. Sassan da abin ya shafa na gwamnatin kasar Sin sun taba kafa "kungiyoyin yin ziyara ta manyan Panda" wadanda suka je kasashen waje don yin "ziyara" wato yin nuni har fiye da sau 10.

A ran 11 ga watan Maris na shekarar 1999, gwamnatin tsakiya ta ba wa yankin musamman na Hongkong kyautar manyan Panda guda 2 masu suna "Jiajia" da "Anan", gwamnatin yankin ta ware kudin Hongkong Yuan miliyan 80 domin gina wani dakin kiwon manyan Panda na musamman. Yanzu, wadannan manyan Panda guda 2 suna nan suna cikin zaman jin dadi a Hongkong, sun samu kauna sosai daga wajen mutanen Hongkong.

Babbar Panda dabba ce ta tsohon zamani wato zamanin da wata irin dabbar da ake kira dinosaur ke zama rayuwarsu a duniya, bayan da ya shafe shekaru fiye da miliyan 3 yana ta yin hahayayyafa har zuwa yanzu, sabo da haka ya zama "fossil" din dabbobi. Yanzu yawan manyan Panda na daji ya kai fiye da 1590 kawai a duk duniya, ya zuwa karanshen shekarar 2004, yawan manyan Panda da mutanen ke kiwonzu ya kai 163. (Umaru)