 A ran 12 ga wata majalisar wucin gadi ta Iraki ta zartas da gyararren shirin tsarin mulkin kasar, an yarda da cewa za a kara rubuta abubuwan da suka shafi yarjejeniyar da aka daddale kafin wannan lokaci tsakanin kukunoni daban-daban kan batun tsarin mulkin, ta yadda za a kau da siratsi domin zartas da sabon tsarin mulki da za a yi a ran 15 ga wannan wata ta hanyar jefa kuri'ar raba gardama.
A wannan rana da dare, daga cikin 'yan majalisa 275 na majalisar wucin gadi ta Iraki, da akwai 157 wadanda suka halarci taron musamman na majalisar wanda aka shefe sa'I daya ana yin sa don tattauna gyararren shirin tsarin mulkin da aka tsara bisa yarjejeniyar da aka daddale a ran 11 ga wata tsakanin kurunoni daban-daban kan batun tsarin mulkin. A gun taron Hajem al-Hassani, shugaban majalisar wucin gadi ya sanar da cewa, majalisar ta zartas da gyararren shirin sabon tsarin mulki kai tsaye wato ba tare da jefe kuri'a ba.
Bisa labarin da aka bayar an ce, bisa rokon da rukunin Sunni ya yi, an kara wasu sabbin abubuwa cikin gyararren shiri na sabon tsarin mulki. Da farko an kara wani tsari cewa "wannan tsarin mulki ya tabbatar da dinkuwar kasar Iraki daya". Na 2, an kara wani tsarin cewar "za a yi amfani da yaren Larabaci da na Kurd a shiyyar Kurdistan." Na 3 kuma cikin gyararren shirin tsarin mulkin an kara wani tsari mafi muhimmanci wato shi ne, za a kafa kwamitin musamman cikin watanni 4 na bayan zaben majalisar da za a yi a karshen wannan shekara, kwamitin nan yana da ikon sake dudduba da yin gyare-gyare ga tsarin mulkin, kuma zai gabatar da gyare-gyaren da suka yi ga majalisar kasa don a jefa kuri'a, kuma ba za a iya zartas da shi ba, face sai an samu yawancin kuri'u masu nuna goyon baya.
Kafin wannan rukunin Sunni ya dauka cewa tsarin mulkin da rukunin Shi'a da mutanen Kurdawa suka tsayar ba shi da adalci, kuma ya kirayi jama'a 'yan rukunin da su jefa kuri'ar nuna kin yarda a lokacin jefa kuri'ar raba gardama da za a yi a ran 15 ga wannan wata. Domin daidaita hargitsin da ake yi dangane da tsarin mulki, kwanan baya shugabannin rukunin 'yan darikar Shiia da na Kurdawa sun sake yin shawarwari a tsakaninsu da shugabannin rukunin Sunni. Bayan shawarwarin da aka yi cikin tsanani a tsakanin wadannan rukunonin 3, a ran 11 ga wata kuma an samu ra'ayi daya, wato an yarda da cewa bayan da aka zartas da tsarin mulki ta hanyar jefe kuri'ar raba gardama, kuma za a iya yin masa gyare-gyare, ta yadda za a dakatar da gardamar da ake yi yanzu a tsakanin rukunoni daban- daban kan abubuwan da ke cikin tsarin mulki don kiyaye yunkurin farfado da Iraki a fannin siyasa.
Bayan da rukunoni daban-daban suka yi sulhuntawa kan matsalar tsarin mulki, Jalal Talabani, shugaban gwamnatin wucin gadi ta Iraki ya bayyana cewa, wannan ya zama wata yarjejeniya "mai ma'anar tarihi", wadda ba ma kawai ta cika bukatar rukunin sunni ba, hatta ma ta samu karbuwa daga wajen muhimman kungiyoyin siyasa daban-daban na majalisar kasar, sabo da haka rukunoni daban-daban na Iraki dukkansu ba su da dalilin yin adawa da shi.
Manazarta sun bayyana cewa, a gabannin jefar kuri'ar raba gardama da za a yi a kasar Iraki, muhimman rukunoni wato rukunin Shiite da na mutanen Kurd da na Sunni sun daddale yarjejeniya kan matsalar tsarin mulki, kuma gwamnatin wurin gadi ta tabbatar da gyararren shirin tsarin mulkin, sabo da haka an kara yiwuwar zartas da sabon tsarin mulki ta hanyar jefa kuri'ar raba gardama. (Umaru)
|