A ran 12 ga watan nan da safe kasar Sin ta yi nasarar harba kumbo dan sama janati mai lamba Shenzhou 6 da ke dauke da mutane. Wannan shi ne karo na biyu da kasar Sin ta yi nasarar harba kumbo dan sama janati mai daukar mutum a cikin shekaru 2 da suka shige. Yanzu sai ku saurari labarin da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya ruwaoto mana daga wurin da aka harba kumbo dan sama janati. Yau karfe 9 da safe, bayan da aka bayar da umurnin kunna wuta, sai roka mai tsawon mita 60 ya amai jan wuta, a cikin babban sauti ne ya kai kumbo dan sama janati mai lamba Shenzhou 6 ya tashi daga kasa zuwa samaniya!
Wannan kumbo dan sama janati an harba shi ne daga cibiyar harba tauraron dan Adam na Jiuquan a arewa maso yammacin kasar Sin, kuma yana dauke da mutane biyu na kasar Sin, zai yi zirga zirga a kwanakin baya. A kwanakin nan za su yi waya da kasa. Bayan da suka kamala aikinsu za su dawo wani filin da ke a jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin da firayim minista Wen Jiabao na majalisar gudanarwa ta kasar Sin sun kallaci yadda aka harba wannan kumbo dan sama janati. Bayan minti 40 da aka harba kumbon nan, Mr. Chen Bingde, babban kwamanda na aikin zirga zirgar kumbo dan sama janati mai daukar mutum na kasar Sin ya sanar da cewa, an samu cikakkiyar nasara a wajen harba kumbo dan sama janati mai lamba Zhenzhou 6. Hu Jintao da Wen Jiabao da sauran shugabannin sun taya su murna. Firayim minista Wen Jiabao ya yi jawabi a cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiu Quan ta kasar Sin . ya ce, Kasar Sin ta yi gwaje gwajen kimiyar harba kumbo dan sama janati ne duk sabo da makasudin zaman lafiya, kuma taimako ne ga kimiya da sha'anin zaman lafiya na 'yan Adam. Muna son gama kai da jama'ar duniya a wajen yin amfani da samararin sama sabo da makasudin zaman lafiya. Nasarar harba wannan kumbo dan sama janati tana da muhimmancin gaske, ta zama wani muhimmin taki ga wannan tafiyar kumbo dan sama janati. Ina fatan wannan tafiyar kumbo dan sama janati zai samu cikakkiyar nasara.
An bayyana cewa, a yayin da wannan kumbo dan sama janati ke zirga zirga, matuka za su yi gwaje gwjen kimiya iri iri, ciki har da renon iri da hada kayayyaki, ban da haka kuma za a bincike maganganu na likitanci.
Matukan wannan kumbo dan sama janati su ne wadanda aka zaba daga mutane da yawa, su ne Fei Junlong mai shekaru 40 da haifuwa da Ni Haishen mai shekaru 41 da haifuwa. Sun ce, babban burinsu shi ne samun cikakkiyar nasara a cikin zirga zirgar wannan kumbo dan sama janati. (Dogonyaro)
|