Har zuwa ran 10 ga watan nan, a cikin kwanaki 3 kawai, an sha samun hare-hare da garkuwar da aka yi wa ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na Kawancen Kasashen Afirka wato AU a yankin Darfur na kasar Sudan, wanda ya sake jawo damuwar mutane game da makomar yin shawarwarin zaman lafiya na karo na 6 da ake yi.
Yanzu kungiyar AU ta girke sojojin kiyaye zaman lafiya kimanin dubu 6 a yankin Darfur na kasar Sudan, wadanda suke sa ido kan gwamnatin kasar Sudan da dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka daddale a watan Afril na shekarar da ta gabata. Harin da aka kai wa sojojin kare zaman lafiya na kungiyar AU a ran 8 ga watan nan hari ne na karo na farko tun bayan da suka girke a Darfur, wanda ya zama sanadiyar mutuwar sojoji 3, yayin da direbobi 2 suka ji rauni. Kungiyar AU ta bayar da sanarwar gaggawa a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya a ran 9 ga wata, inda a bayyane ne ta la'anci kungiyar Sudan Liberation Movement da ya kamata ta dauki nauyin lamarin nan bisa wuyanta.
Bisa wani labari daban da aka bayar, an ce, kakakin kungiyar AU da ke kasar Sudan Noureddine Muzni ya ba da sanarwa a birnin Khartum, hedkwatar kasar Sudan a ran 10 ga wata cewa, dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar da ke yankin Darfur sun saki sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU 36, amma sun yi garkuwa da sojoji 2.
Bayan da matsalar Darfur ta barke a watan Fabrairu na shekarar 2003, dakarun Sudan Liberation Movement da the Justice and Equality Movement da farar hula bakar fata na wurin suka kafa sun fara yin fama da gwamnatin kasar Sudan a fili, sun bukaci su taifyar da harkokin yankinsu da kansu, da kuma kafa wata sabuwar kasa. Saboda aikin daidaitawa da kasashen duniya suka yi, gwamnatin kasar Sudan da dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar sun yi shawarwarin zaman lafiya sau 5 gaba daya. Duk da haka, ba a sami ci gaba na a-zo-a-gani kan muhimman abubuwa, kamar sa aya ga yake-yake ba. An bude shawarwarin zaman lafiya na karo na 6 a birnin Abuja a ran 15 ga watan jiya, an fara yi tattaunawa kan muhimman batutuwan da ke kunshe da more iko da dukiya da kuma tsaron kai a wannan wata.
A cikin irin wannan halin da ake ciki, dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar Sudan da ke Darfur sun tayar da rashin kwanciyar hankali, nufinsu shi ne matsa wa gwamnatin kasar Sudan da ke halartar shawarwarin zaman lafiya lamba, don neman samun moriya mafi girma a cikin shawarwarin. Game da kungiyar dakarun da ta yi garkuwa da sojojin kare zaman lafiya na kungiyar AU, wani jami'in kasar Sudan na wurin ya yi bayani cewa, wannan kungiyar dakaru tana son ta nuna wa kowa cewa, tana fatan za su shiga shawarwarin zaman lafiya da ake yi a birnin Abuja, don neman samun moriyarta a cikin gwamnatin kasar Sudan na nan gaba.
Masu nazarin harkokin yau da kullum sun bayyana cewa, ko da yake hare-hare da garkuwa da aka sha samu a yankin Darfur a kwanan baya sun ba da tasiri maras kyau kan shawarwarin zaman lafiya da ake yi a yanzu, amma ya kamata mu gano cewa, a halin yanzu dai, kasar Sudan tana nan tana bin hanyar sassauci da sulhuntawa. Shugaban kasar Sudan Omar el-Bashir da shugaban kungiyar Sudan Liberation Movement na lokacin nan marigayi John Garang sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya daga duk fannoni a watan Janairu na shekarar da muke ciki, an sa aya ga yakin basasa na tsawon shekaru 21 a kudancin kasar. A watan Satumba gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar Sudan ta yi rantsuwar kama aiki. Tabbatar da zaman lafiya a tsakanin kasar Sudan ta arewa da ta kudu ya samar da sulhuntawa da zaman lafiya ga shawarwarin zaman lafiya kan matsalar Darfur. Shi ya sa ko da yake ya zuwa yanzu shawarwarin zaman lafiya kan matsalar Darfur yana fuskantar kalubale iri daban daban, amma mutane suna fata kuma sun yi imanin cewa, a sakamakon sa hannu da aikin sulhu da kungiyar AU ta yi, bangarori 2 da ke da hannu cikin shawarwarin zaman lafiya kan matsalar Darfur ta Sudan za su iya kawar da cikas, za su warware matsalar nan da kasar Sudan take damuwa da ita har cikin dogon lokaci.(Tasallah)
|