Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-12 15:36:58    
Za a harba kumbo mai daukar mutane kuma mai lamba 6 mai suna Shenzhou na kasar Sin a nan gaba kadan

cri
A ran 11 ga wata, kamfanin dillancin labaru na hukumar kasar Sin wato kamfanin Xinhua ya ba da wata sanarwa cewa, a ran 12 ga wannan wata, za a harba kumbo mai daukar mutane mai suna Shenzhou na 6 daga cibiyar harba kumbo ta Qiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Wannan kumbo zai dauki 'yan sama jannati 2 wadanda za su tafiyar da ayyukansu cikin kwanaki da yawa. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayani game da wannan labari.

Sanarwar da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar ya ce, ran 11 ga wata jami'in hedkwatar ba da umurni ga aikin zirga-zirgar kumbo mai daukar mutane ta kasar Sin cewa, bisa shirin da aka tsayar za a harba kumbo mai daukar mutane mai lamba 6 kuma mai suna Shenzhou daga cibiyar harba kumbu ta Qiuquan kasar Sin, bayan da aka kammala ayyukan da aka tsayar, za a dawo da shi a muhimmin filin saukar kumbu na jihar Mongoliya ta gida da ke arewacin kasar Sin. Yanzu ana nan ana yin ayyuka daban-daban domin shirin harbar wannan kumbo lami lafiya.

An fara aikin zirga-zirgar kumbu mai daukar mutane na kasar Sin daga shekarar 1992, kuma ana yin wannan aiki cikin matakai 3. Mataki na farko shi ne harba kumbo maras dauke da mutane da na daukar mutane wadanda suka aika da 'yan sama jannati zuwa hanyar da aka tsara a sararin sama, da yin bincike da gwaje-gwajen kimiyya, kuma an dawo da 'yan sama jannati lami lafiya. An riga an kammala wannan mataki tun kafin shekaru 2 da suka wuce, wato an harba kumbo mai daukar mutane kuma mai lamba 5 mai suna Shenzhou kuma an dawo da shi lami lafiya. Aikin da aka yi cikin mataki na 2 shi ne, ci gaba da kyautata fasahar zirga-zirgar kumbu mai daukar mutane, kuma 'yan sama jannati sun fita daga kumbu don yin tafiya a sararin sama, da harba ofishin yin gwaje-gwaje na sararin sama. Mataki na 3 kuma shi ne, kafa tashar sararin sama na dindindin.

Kwanan baya yayin da Mr. Wang Yongzhi, babban mai tsara fasalin aikin zirga-zirgar kumbu mai daukar mutane na kasar Sin ya amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa ya bayyana cewa, "Kumbun da za a harba a wannan gami zai dauki 'yan sama jannati 2 kuma zai yi tafiyar kwanaki da yawa a sararin sama, kuma za su yi fito daga dakin da za a dawo da shi kuma su shiga cikin dakin da ake sarrafa shi domin ci gaba da tafiya bisa hanyar sararin sama, da yin muhimman gwaje-gwajen sararin sama."

Kwanan baya yayin da Mr. Hu Sixiang, mataimakin babban jami'I mai kula da ayyukan zirga-zirgar kumbu mai daukar mutane na kasar Sin ya amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin ta zama kasa ta 3 wato bayan Amurka da Rasha wajen sarrafa fasahar zirga-zirgar kumbo mai daukar mutane. Ko da yake an fara aikin zirga-zirgar kumbo mai daukar mutane na kasar Sin ba da dadewa ba, amma aikin yana da muhimmiyar ma'ana ga ciyar da tattalin arziki da kimiyya da fasaha gaba. Ya ce,"Aikin zirga-zirgar kumbo mai daukar mutane yana da babbar ma'ana wajen siyasa da tattalin arziki da kimiyya da fasaha, ya zama alama ce ga karfin wata kasa daga duk fannoni. Wannan aiki ya ba da taimako irin na jagoranci ga sana'o'I da yawa, alal misali, wannan aiki yana bukatar kimiyya da fasaha na zamani, shi ya sa ya sa kaimi ga sana'o'I daban-daban na fannin kimiyya. (Umaru)