Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-12 09:54:42    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(6/10-12/10)

cri
Kwamitin wasan Olympic na kasar Sin ya ba da sanarwa a ran 9 ga watan Oktoba cewa, shugaban kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa Jacques Rogge zai kawo wa kasar Sin ziyara daga ran 11 zuwa ran 16 ga watan Oktoba. A lokcin ziyararsa a kasar Sin, Mr. Rogge zai halarci bikin bude wasannin duk kasar Sin na karo na 10 da za a yi a birnin Nanking da ke gabashin kasar Sin, zai kuma ziyarci Beijing da Qingdao don dudduba ci-gaban gina filayen wasa da za a yi amfani da su a wasannin Olympic na shekarar 2008.

Darektan sashen wasanni na Hadaddiyar Kungiyar Wasan Judo ta Kasa da Kasa kuma wakilin fasaha na wasan judo na wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 Mr. Francois Besson ya duba filin wasan judo da ke nan Beijing a kwanan baya, ya kuma yi kallo gasannin judo na wasannin duk kasar Sin na karo na 10 da aka yi a birnin Nanking na gabashin kasar. Mr. Besson ya bayyana cewa, ayyukan shirya gasannin judo na wasannin duk kasar Sin na karo na 10 suna da kyau kwarai, haka kuma ya gamsu da ci gaban gina filayen wasa da za a yi amfani da su a wasannin Olympic na Beijing, ya yi imanin cewa, tabbas ne za a ci babbar nasarar shirya gasannin judo na wasannin Olympic na Beijing.

An kafa kwamitin fasahar hawan doki na kwamitin shirya wasannin Olympic na lokacin zafi na karo na 29 a hukunce a Hong Kong a ran 5 ga wata. Gwamnan yankin musamman na Hong Kong Donald Tsang ya dauki nauyin uban tafiya bisa wuyansa, kuma an danka wa Mr. Rafael Hui, daraktan harkokin ayyukan gwamnatin yankin musamman na Hong Kong nauyin shugaban wannan kwamiti. A watan Yuli na shekarar da muke ciki, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Olymipic ta Duniya ya tsai da kudurin canja wurin gasannin fasahar hawan doki na wasannin Olympic da na nakasassu daga Beijing zuwa Hong Kong.

A kwanakin nan, hukumar kula da kungurmin daji ta kasar Sin ta sanar da cewa, lardin Shanxi ya yi shekaru fiye da 5 yana bakin kokarinsa wajen daidaita rairayin da fadinsa ya kai muraba'in kilomita fiye da dubu 6 gaba daya. Kungurmin daji da filaye masu ciyayi da aka kara dasa za su kiyaye birnin Beijing da zai yi wasannin Olympic a shekarar 2008 daga iska mai karfi da rairayi.

An ci gaba da yin gasannin zagaye na farko don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin Duniya na wasan kwallon kafa na kasar Jamus na shekarar 2006 a nahiyoyi daban daban a ran 8 ga watan nan. A ran nan kungiyoyn wasan kwallon kafa guda 14 sun sami damar shiga gasar cin kofin Duniya na wasan kwallon kafa na kasar Jamus da za a yi a shekara mai zuwa. A cikinsu kuma, kungiyoyin kasashen Togo da Angola da Cote d'Ivoire da kuma Ghana za su shiga wannan muhimmiyar gasar wasan kwallon kafa a karo na farko. A halin yanzu, kungiyoyin wasan kwallon kafa guda 24 da ke kunshe da kungiyar kasar Jamus da ta bakonci wannan gasa sun sami damar shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa.(Tasallah)