Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-11 16:25:20    
A kan samu zumunci mai danko a cikin masifa

cri
Girgizar kasa mai tsanani da ya faru a kudancin Asia ta kawo wa kasar Pakistan da kasar India da shiyyar Kashimir babbar hasarar rayuka da dukiya, kuma ta jawo hankalin zaman tarayyar kasashen duniya. Ya zuwa ran 10 ga watan nan, mutane dubu 20 sun mutu, mai yiwuwa ne yawan mutanen da suka mutu zai karu. A gaban wannan babbar masifa kasar India da kasar Pakistan da suka sha bala'I sun nuna halin mutumtaka mai daukaka, sun hada kansu a wajen kau da bala'i. Wannan girgizar kasa mai tsanani ta zama muguwar masifa ga kasashen nan biyu, amma ta zama wata dama mai kyau ta kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Yanzu sai ku saurari wani sharhin da aka yi.

A cikin girgizar kasa da aka yi kasar Pakistan ta fi shan bala'i. Bayan da aka yi girgizar kasa sai kasar India ta nuna wa Pakistan taimako. A ran 8 ga watan nan da dare, firayim ministan kasar India ya buga wa shugaba Musaraf na kasar Pakistan don nuna juyayi ga kasar Pakistan sabo da babbar hasarar da aka yi a cikin wannan bala'in girgizar kasa, kuma ya nuna cewa, za ta gabatar wa Pakistan gudummuwa da taimakon da kasar Pakistan ke bukata. Wannan aiki sosai ya nuna sahihancin kasar India. Shugaba Musaraf na kasar Pakistan ya nuna wa firayim ministan kasar India godiya, kuma ya nuna cewa, idan kasar kasar Pakistan tana bukatar taimako zai buga masa waya. A shiyyar Kashimir da aka yi girgizar kasa mai tsanani, kwamandoji da sojoji na kasashen biyu sun yi taro don nuna wa juna taiamko.

Dalillin da ya sa kasar India da kasar Pakistan su hada kai don yin fama da bala'I shi ne sabo da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi ta kyautatuwa. Kasar India da kasar Pakistan muhimman kasashe biyu ne a kudancin Asia, amma ba su da sulhu tun dogon lokaci, har sun yi tasiri ga zaman lafiya da zama mai dorewa na shiyyar nan. A cikin shekaru gommai da suka shige ba a taba dakatar da bude wuta a tsakanin bangarorin biyu ba. Bayan da aka shiga cikin karni na 21, shugabannin bangarorin biyu sun yi ta yin shawarwari don kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tun daga watan Febrairu na shekara ta 2004, kasashen biyu sun shirya shawarwari na shimfida zaman lafiya har sau da yawa. A watan Satumba na bana, firayim ministan kasar India da shugaban kasar Pakistan sun yi saduwa a gun taron shugabannin MDD da aka yi a New York. A farkon watan nan ministocin harkokin waje na kasashen biyu sun yi saduwa, inda duk sun nuna burinsu na ci gaba da yin tattaunawa a duk fannoni, kuma za su yi kokarin daidaita maganar Kashmir.

Abin da ya fi jawo hankalin mutane shi ne, hadin kai da India da Pakistan suka yi a wajen kau da bala'in girgizar kasa zai kara amincewa juna a tsakanin jama'ar kasashen biyu, kuma zai kara sa kaimi ga ci gaban aikin shimfida zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Lallai wannan alheri ne ga jama'ar kasashen biyu har ma ga jama'ar kasashen shiyyar nan gaba daya. (Dogonyaro)