Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-07 17:42:14    
Kasar Sin tana kara bude wa kasashen waje hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama sannu a hankali

cri
Babbar hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama masu daukar fasinja da kayayyaki ta kasar Sin ta bayyana a kwanakin baya cewa, za ta bude hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama masu daukar fasinja da kayayyaki ga kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasashen waje, don sa kaimi ga bunkasa harkokin zirga-zirgar jiragen sama da na tattalin arzikin yammacin kasar Sin. Wannan ya zama wani kuduri ne mai muhimmanci da kasar Sin ta tsai da don bude wa kasashen waje hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama. Yanzu, kasar Sin tana gudanar da ayyukan bude wa kasashen waje hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama sannu a hankali.

Sabo da ta hanyar bude wa kasashen waje hanyoyin zirga-zirgar jiragem sama masu daukar fasinja da kayayyaki, za a sami babban taimako wajen sa kaini ga yin ma'amala tare da kasashen waje da bunkasa harkokin tattalin arzikin wuri-wuri, shi ya sa babbar hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin ta tsai da kuduri kan bude wa kasashen waje hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama a wurare da ke yammacin kasar Sin. Malam Zhang Zengming, kakakin babbar hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin ya bayyana cewa, "nan gaba idan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasashen waje sun nemi kasar Sin da ta bude musu hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama a birane da ke yammacin kasar Sin, to, za mu yi kokari sosai wajen taimake su."

Babban dalilin da ya sa babbar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin ta tsai da kudurin bude wa kasashen waje hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama shi ne domin, a sakamakon ci gaba da ake samu wajen aiwatar da manyan tsare-tsaren raya wurare da ke yammacin kasar Sin, an bunkasa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma da sauri a wadannan wurare, sa'an nan kuma yawan fasinjoji da kayayyaki da jiragen sama ke daukawa yana ta karuwa da sauri sosai. A cikin irin wannan hali ne, an bukaci a kara daga matsayin zirga-zirgar jiragen sama masu daukar fasinja da kayayyaki. Bisa labarin da aka bayar, an ce, lardin Sichuan da na Yunnan da Huizhou da jihar Guangxi da ta Tibet da birnin Zhongqing wadanda ke kudu maso yammacin kasar Sin su ne wurare na farko da za a bude wa kasashen waje hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama a wurare da ke yammacin kasar Sin. Wato za a yarda da jiragen sama na kasashen waje da su yado zango a wadannan wurare, kana su tashi zuwa sauran kasashe.

Kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasashen waje da yawa suna sha'awar mataki da kasar Sin ke daukawa wajen bude musu hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama sannu a hankali. Malam Zhang Yimeng, jimi'in ofishin kamfanin zirga-zirgar jiraren sama na kasar Holland da ke a kasar Sin ya ce, "wannan wani albishiri ne ga kamfaninmu na zirga-zirgar jiragen sama na kasashen waje, kuma ya ba mu babbar dama. Ya kamata, mu yi amfani da damar nan a tsanake. "

Bisa wani labarin dabam da aka bayar, an ce, yanzu, babbar hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin tana nan tana la'akari da bude wa kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasashen kungiyar ASEAN manyan filayen jiragen sama sannu a hankali a wurare da ke mashigar teku na Kogin Zhujiang da ke a kudu maso gabashin kasar Sin, an kuma fi samu ci gaba a fannin tattalin arziki a wadannan wurare. Makasudin yin haka shi ne domin sa kaimi ga kara karfin hadin guiwa tsakanin wadannan wurare da kasashen kungiyar ASEAN a fannin yawon shakatawa da tattalin arziki da sauransu.  (Halilu)