Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-05 17:25:16    
Kasar Sin za ta zama kasar yawon shakatawa mafiya girma a duniya a shekarar 2020

cri
A kwanakin baya yayin da malam Sun Gang, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ya karbi ziyarar da manema labaru suka yi masa, ya hakake cewa, kasar Sin za ta zama kasar yawon yawon shakatawa mafiya girma a duniya a shekarar 2020. Sabo da haka kasar Sin za ta yi kokari sosai wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa a gida, kuma za ta kara yin ma'amala da hadin guiwa a tsakaninta da kasashe daban daban a fannin yawon shakawata, don ba da taimako wajen gaggauta bunkasa harkokin yawon shakatawa a Sin da duniya.

Kasar Sin tana daya daga cikin kasashe da suka fi samu ci gaba da sauri wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa a duniya. A karshen shekarun 1970, yawan baki 'yan kasashen ketare wadanda suka zo kasar Sin don yin yawon shakatawa ya kai miliyan 1.8 kawai, amma ya zuwa shekarar bara, yawan nan ya riga ya wuce miliyan 100.

Yayin da manema labaru suka ziyarci Mr Porras Olalla, jami'in hukumar yawon shakatawar kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya don jin ta bakinsa, sai ya bayyana cewa; "hukumar yawon shakatawar kasa da kasa ta kiyasta cewa, kasar Sin za ta kai matsayi na farko a duniya wajen samun yawan masu yawon shakatawa daga kasashen waje a shekarar 2020, sa'an nan kuma yawan mutanen Sin da za su yi yawon shakatawa a kasashen waje ma zai kai matsayi na hudu a duniya. Sabo da haka kasar Sin za ta kara ba da babban taimakonta wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa a duniya. Hukumarmu ma za ta kara lura da harkokin yawon shakatawa da ake yi a kasar Sin."

Dangane da wannan kiyastarwa da hukumar yawon shakatawar kasa da kasa ta yi, Malam Sun Gang ya hakake cewa, " Yanzu mun riga mun mayar da wannan kiyastarwa bisa manufar da muke neman tabbatarwa. Bisa halin a ake ciki yanzu, mun hakake cewa, za mu cim ma manufar nan. "

Yanzu, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ta riga ta tsara wani kasafin bunkasuwar harkokin yawon shakatawa filla-filla don neman tabbatar da manufar nan. A karkashin wannan kasafi, yawan baki 'yan kasashen ketare wadanda za su yi yawon shakatawa a kasar Sin zai wuce miliyan 200 a shekarar 2020, yawan kudin musanya da kasar Sin za ta samu daga wajen aikin yawon shakatawa zai wuce dalar Amurka biliyan 58. Haka nan kuma yawan mutanen Sin da za su yi yawon shakatawa a gida zai wuce biliyan 2.9, sa'an nan yawan kudin shiga da za a samu daga wajen aikin yawon shakatawar nan zai wuce kudin Sin Yuan biliyan 2000. Malam Sun Gang ya bayyana cewa, nan gaba yayin da kasar Sin ke yin kokari sosai wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa a gida, kuma za ta kara yin ma'amala da hadin guiwa a tsakaninta da kasashe daban daban a fannin yawon shakatawa. Ya ce, "ya kamata, mu kara gudanar da harkokin yawon shakatawa da kyau a wurare daban daban na kasar Sin, sa'an nan kuma mu kara yin ma'amala da hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashe daban daban a fannin yawon shakatawa, don ba da taimako sosai wajen gaggauta bunkasa harkokin yawon shakatawa a gida da duniya."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an yi ta kara yin ma'amala da hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashe daban daban a fannin yawon shakatawa. Ya zuwa shekarar 2004, yawan kamfanonin yawon shakatawa da 'yan kasuwa na kasashen ketare suka kafa bisa jarinsu ya kai 5, haka nan kuma yawan kamfanonin nan da 'yan kasuwa na gida da waje suka kafa cikin hadin guiwarsu ya kai 13. Bisa alkawarin da kasar Sin ta dauka yayin da aka shigar da ita cikin kungiyar ciniki ta duniya, kasar Sin tana gaggauta bude wa kasashen wajen kofar yawon shakatawa. (Halilu)