Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-05 17:21:02    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(29/9-05/10)

cri
A ran 28 ga watan Satumba, a nan birnin Beijing, an kafa kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin wadda za ta shiga wasannin kasashen gabashin Asiya na karo na hudu. Kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin tana kunshe da mutane 567, ciki har da 'yan wasa guda 399 wadanda za su shiga gasanni 16 ban da gasar karate a cikin wasannin kasashen gabashin Asiya na karo na hudu. Za a yi wasannin kasashen gabashin Asiya na karo na hudu a birnin Macao na kasar Sin daga ran 29 ga watan Oktoba zuwa ran 6 ga watan Nuwamba.

A ran 29 ga watan Satumba, wato an raga sauran misalin kwanaki 30 da za a bude wasannin kasashen gabashin Asiya na karo na hudu, an yi harkar ba da wutar yola ta wasannin a birnin Macao na kasar Sin domin maraba da budewar wasannin. A gaban kofar babban ginin gwamantin shiyyar musamman ta Macao, gwamnan shiyyar Ho Hau Wah shi da kansa ya kunna wuta da za a mika ta har zuwa filin wasanni na Macao.

A ran 2 ga watan nan, an rufe wasan fid da gwani kan kokawa na duniya na na shekara ta 2005 a birnin Budapest, babban birnin kasar Hungary. A cikin gasa ta kwanaki bakwai, 'yan wasa na kasar Sin sun samu lambobin zinariya 2 da azurfa 2 da tagulla 1, ta haka kungiyar kasar Sin ta sami matsayi na uku wajen samu lambobin yabo. Kungiyar kasar Rasha ta zama kan gaba bisa lambobin zinariya 5 da azarfa 1 da tagulla 3 da ta samu, kuma kungiyar kasar Japan ta sami matsayi na biyu bisa lambobin zinariya 4 da azarfa 1 da tagulla 1 da ta samu.

A ran 2 ga watan nan, a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, an rufe budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta duniya ta shekara ta 2005 wadda aka shafe kwanaki 8 ana yinta. A cikin karon karshe na gasa ta tsakanin mace da mace, 'yar wasa ta kasar Sin Yan Zi ya lashe Nuria Llagostera Vives, 'yar wasa ta kasar Spain biyu ba ko daya, ta haka ta zama zakara.

A cikin kwanakin nan da suka wuce, a ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Greece, Madam Bakoyannis, magajiyar birnin Athens ta mika wa 'yan wasa na kasar Sin da suka zama zakara a cikin wasannin Olympic na Athens lambar 'yan birnin Athens da aka daukaka sunayensu. Kuma Madam Bakoyannis ta bayyana cewa, tana jin alfahari da 'yan wasa na Sin suka samu lambobin zinariya a cikin wasannin Olympic, kuma tana fatan wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008 zai ci nasara sosai.

A ran 2 ga watan nan, a cikin karon karshe na gasar fid da gwani ta wasannin kwallon kafa a tsakanin matasa 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa da aka shirya a kasar Peru, kungiyar kasar Mexico ta lashe kungiyar kasar Brazil uku ba ko daya, sabo da haka a karo na farko ne ta zama zakara a cikin gasar, kuma kungiyar kasar Brazil ta zo na biyu. Haka kuma a cikin gasar neman samu matsayi na uku, kungiyar kasar Holland ta kashe kungiyar kasar Turkey da ci biyu da daya, shi ya sa ta zo na uku.

To, jama'a masu sauraro, karshen shirin nan na ' wasannin motsa jiki' ke nan, sai ran Laraba mai zuwa, idan Allah ya kai mu. Ni Bello da na gabatar nake cewa, ku huta lafiya.(Kande Gao)