A shekara ta 1993 wani masani da ake kira shi William Rees Mogg ya gano wani littafi mai suna Lunyu da aka fassara da turanci a shekara ta 1691.Wannan littafi ne na darikar Confucius da aka fassara tun tuni.An fassara shi ne daga littafi na Faransanci,littafin Faransanci daga littafin harshen Latin ne aka fassara.A cikin gabatarwar littafin nan an ce "darikar Confucius tana da haske ba iyaka".Limamai na darikar Catholika da suka zo daga kasashen yamma ne sun kasance na farko wajen gabatar da darikar Confucius zuwa kasashen yamma a zamanin daular Ming da ta Qing.Wadannan limamai sun fassara Kong Fu-tsu na sinanci zuwa Confucius na harshen Latin.Har yanzu dai ana amfani da wannan kalma Confucius.Limami Limadou na kasar Italiya ya yi zama na tsawon shekaru 27 a kasar Sin,ya fassara littafin "Lunyu" daga sinanci zuwa harshen Latin.A shekara ta 1687 an buga shi a birnin Paris na kasar Faransa,daga baya an fassara shi zuwa sauran harsuna na kasashen yamma.Daga nan darikar Confucius yana yaduwa a kasashen yamma a kalla dai shekaru dari uku ke nan a yau.
Wadannan limamai sun zo kasar Sin tare da nufin yadada addinansu.bayan isowarsu a kasar Sin,tunanin Confucius ya jawo hankulansu,sun kasha lokuta da dama wajen fassara littattafan Confucius da gabatar da tunaninsa ga kasashen yamma.Mista James Legge yana daya daga cikinsu ya kashe shekaru gomai wajen fassara shahararrun littattafai masu daraja na kasar Sin
Bayan darikar Confucius ta fara yaduwa a kasashen yamma,an dauki mallam Conficius a matsayin masana ilmin falfasa Socrates da plato na tsohon zamani na kasar Greek.Mista Mogg ya ce mallam Confucius " babban mutum ne wajen sanya tubalin wayin kai",ya rubuta wani bayani cewa "har wa yau dai ana aiwatar da abin da ya fada",a cikin bayanin nan ya ce "koyarwar Confucius abu ne na duk Bil Adama,kamar Shakespeare,dukkansu suna da ilimin falfasa da ake iya aikatarwa,suna amincewa da zaman jituwa da bambancin matsayin tsakanin mutane da bin darikar kishin kasa."
A karni na goma sha takwa an fara tattaunawar darikar Confucius a tsakanin masana na Turai ko darikar Confucius ilimi ne talakawa.Tattaunawar nan ta shafe shekaru sama da dari.Bayan da aka yi tattaunawa,masanan Turai sun sane da darikar Confucius.A karni na 20,an sami wani tashe na nuna girmamawa ga Confucius a kasashen yamma.A shekarun sittin na karni na 20,darikar Confucus ta shiga cikin talakawa daga masana falfasa.Wani lokaci mutane da yawa a kasashen yamma suna kishin al'adun gabas,ko talakawa ma su kan yi amfani da maganar "Confucius say" tare da dariya.Ga shi a yau yawancin mutanen kasashen yamma suna girmamawa Confucius.A ganin mutanen kasashen Yamma,darikar Confucius rubutu ne da aka samu babu sunan mawallafi na shi kansa a tarihi,duk da haka Confucius yana daya daga cikin mutane uku na duniya da suka kawo muhimmin tasiri ga wayewar kai na Bil Adama.Littafin "lunyu" da aka samu bayan rasuwar Confucius almajiran Confucius ne suka rubuta. Littafin " muhawara" wanda a ciki an tanadi tunanin mai falfasa Socrates almajirinsa Plato ya rubuta bayan da aka yanke masa hukuncin kisa;littafin "Gospel" wanda ya tanadi maganganu da ayyukan da Jesus,almajiransa ne suka rubuta cikin shekaru gomai da suka gabata bayan da aka kashe shi.
Kafin karni na ashirin,an sami babban cigaba wajen nazarin darikar Confucius a kasashen yamma masu bin addinin Catholic kamar su Italiya da Faransa.An kuma samu babban cigaba wajen nazarin littattafan da takardu na Confucius.Ban da coci har ma a hukumomin nazarin da suka shahara kamar kolejin Faransi ana nazarin darikar Confucius.
A Kasar Britaniya wadda ta fi sauran kasashen duniya cigaban masana'antu da kasuwanci mutane da yawa suna so su samo labarai na game da kasar Sin.Mutane mai tarin yawa sun fara nazarin ilmi na game da kasar Sin.James Legge ya zama profesa na farko a fannin harshen sinanci a jami'ar Oxford wanda ya kashe shekaru da yawa ya fassara shahararrun littattafai na Confucius da na Laozi da na Zhuangzi.Ya yi fassarawa da hankali sosai,ayyukan da ya fassara sun zama wani sakamako mafi nagarta wajen nazarin ilimi na game da kasar Sin a duniyar turanci a karni na 19,har wa yau dai ana amfani da su.Bayan rasuwar James Legge,masana ilimin kasar Sin Mista H.A>Giles da dansa L.Giles na Britaniya sun cigaba da fassara littattafan Confucius haka kuma sun bayar da wasu bayanai kan sakamakon da suka samu kamar bayanin "Confucius da 'yan takararsa".Amurkawa suna matsayin baya wajen nazarin Confucius.Kafin yakin duniya na biyu yawancin masana ilimin kasar Sin na Amurka sun zo ne daga kasar Braitaniya.Bayan yakin duniya na biyu masanan Amurka sun samu babban cigaba wajen nazarin Confucius.(Ali)
|