
Bisa labarin da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya samu,an ce a ran 2 ga wata da sassafe guguwa mai karfi da ake kira "dodo" ta shiga Taiwan ta yi sanadiyar jikkata mutane 37 da mutuwar mutum daya.
A daren ranar nan,cibiyar guguwar dodo ta tafi lardin Fujiang dake kudu maso gabashin kasar Sin,karfin guguwa ya kai digiri 12.domin magance hadari,gwamnatin lardin Fujiang ta kaurar da mutane fiye da dubu 370 daga wurare masu hadari.(Ali)
|