Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-30 16:22:54    
Kasar Sin tana tafiyar da aikin bincike wata lafiya

cri
A ran 29 ga watan nan wakilin gidan rediyon kasar Sin ya ziyarci wani jami'I na cibiyar biancike wata ta ofishin kula da zirga zirgar sararin sama na kasar Sin, inda ya ce, bayan da aka yi shekara daya ana yin aikin wurjanjan, yanzu kasar Sin ta riga ta daidaita maganganun fasahohi na tauraron dan Adam da zai bincike wata, ana yin ayyuka daban daban lafiya, za a harba tauraron dan Adam na bincike wata a karshen shekara ta 2007. yanzu sa ku saurari labarian da aka ruwaito mana.

Tun shekarar bara ne kasar Sin ta fara aikin bincike wata, an yi tsare tsare da shiruruka da yawa. A watan Nowamba na bara, an gama aikin tsara shiri na wannan aiki, an fara yin mudal. A halin yanzu ana gudanar da aikin bincike wata lafiya.

Mr. Gen Yan, jami'in cibiyar wata na ofishin kula da zirga zirgar sararin sama na kasar Sin ya zanta da wakilin gidan rediyon kasar Sin cewa, bayan da aka yi shekara daya ana aikin sabunta gwanintar sana'a, yanzu an riga an daidaita matsalolin fasaha na harba tauraron bincike wata. Duk aiki yana tafiya yadda ya kamada.

Mr. Gen Yan ya bayyana cewa,, an yi model na fasaha duk don yin gwaji, bayan gwaji za a iske matsaloli, in an iske matsala za a daidaita. Bayan da kasar Sin ta gama aikin kera modal na farko, kuma za ta fara aikin kera modar zalla, wato za a bincike da kera tauraron dan Adam da za a harba zuwa sararin samaniya. Bias shirin da aka tsara, kasar Sin za ta harba tauraron bincike wata a karshen shekara ta 2007.

Mr. Ouyan Zhiyuan, dan kimiya na farko na aikin bincike wata na kasar Sin ya ce, ko da ya ke kasar Sin ta yi baya har shekaru da dama a wajen bincike wata idan an kwatanta ta da Amurka da Rasha, amma kasar Sin ta yi gaba a wajen fasahohi. A wajen kimiya akwai wasu ayyukan da ba a taba yi ba.

Shekaru fiye da 40 ke nan da kasar Sin ta fara aikin bincike sararin samaniya, tana da iyawar kera rokoki da taurarin dan Adam ita kanta. Kuma a shekara ta 2003 ne ta harbaa kumbo jannati mai daukar mutum. Kwararru sun bayyana cewa, a halin yanzu kasar Sin ta samu iyawar bincike wata.

A halin yanzu aikin da aka fara shi ne mataki na farko, wato na kewaya wata. Kasar Sin ta kasha kudin kasar Sin Yuan biliyan 1.4 kan wannan aiki na bincike wata.

(Dogonyaro)