Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-29 16:55:57    
Karfin tserereniya na kasashe daban daban a ganin dandalin tattaunawa na duniya a kan tattalin arziki

cri

Kasar Finland

A ran 28 ga wata a birnin Geneva, an bayar da wani rahoto a kan karfin tserereniya na kasashe daban daban daga shekarar 2005 zuwa ta 2006 a gun dandalin tattaunawa na duniya a kan tattalin arziki. Wannan rahoto ya ce, kasar Finland ta kasance lamba daya a cikin shekaru uku da suka gabata; kasashe da yankuna daga lamba biyu zuwa goma su ne: Amurka da Sweden da Danmark da yankin Taiwan na kasar Sin da Singapore da Iceland da Switzerland da Norway da Australiya. Kasar Sin ta zama lamba 49, wadda ta sami rinjaye idan aka kwatanta ita da kasashen India da Brazil da Rasha.

Rahoton ya bayyana cewa, kasar Finland ta fi samun rinjaye ne domin gwamnatin kasar ta sarrafa tattalin arzikinta da kyau kuma ta kara karafafa ingancin hukumomin jama'a. Ban da wannan kuma, kamfanoni masu zaman kansu na kasar suna fi son yin amfani da sababbin fasasha tare da nuna goyon baya ga sababbin al'adu. Ko shakka babu, kasar Amurka kwararriya ce wajen fasasha da sababbin al'adu, amma ba ta kago wani muhallin tattalin arziki mai dorewa ba, har ta zama lamba 47 a fannin, wannan ya bayyana cewa, zaman al'ummar kasashen duniya suna kara damuwar tattalin arzikin kasar Amurka masamman gebin kasafin kudi na gwamnatinta.

A shekarar da muke ciki, kasashe da ke arewacin Turai sun yi kyau sosai. A cikin sauran kasashen Turai, Ireland ta hau lambobi 4 har ta zama lamba 26; kasar Esthonia ta kasace lamba 20 cikin shekaru biyu, ta yadda ta zama kasar da ta fi da karfin tserereniya a cikin kasashe 10 da suka shiga kungiyar EU a shekarar da ta gabata. Amma kasar Girika ta zama lamaba 46 daga lamba 37 a bara, ta yadda ta zama kasar da ba ta da karfin tserereniya ba a cikin kasashe 25 na kungiyar EU tare da kasar Italiya, wadda ta zama lamba 47. Kasar Poland ta hau lambobi 9 har ta zama lamba 51.

Kamar yadda ta yi a bara, a cikin shekarar da muke ciki, kasar Chile ta zama lamba 23, ta yadda ta sami rinjaye sosai idan aka kwatanta ita da sauran kasashen latin Amurka. A shiyyar gabas ta tsakiya da ta arewacin Afirka, kasar Hadaddiyar daular Larabawa ta zama lamba 18, kasar Qatar ta zama lamba 19. ko da yake yawacin kasashen Afirka da ke kudancin Sahara ba su da karfin tserereniyar kasa sosai ba, amma wasu kasashe sun sami ci gaba. Kasar Afirka ta kudu ta zama lamba 42, Botswana ta zama lamba 48, Mauritius ta zama lamba 52, kasar Ghana ta zama lamba 59. A cikinsu kasar Ghana ta fi jawo hankulan mutane a sakamakon hau lambobi tara.

Yankin Taiwan na kasar Sin da kasar Singapore sun fi samun rinjaye a cikin kasashen Asiya, dukkansu sun fi kasar Japan, wadda ta zama lamba 12. Kasashen Sin da India sun zama lamba 49 da 50. kasar Sin ta sauka da lambobi 3, domin ta rage yawan jarin da ta zuba a wasu masana'antu. Amma kasar India ta hau lambobi 5 a sakamakon rinjaye da ta samu a fannin fasasha. Wannan rahoto yana ganin cewa, a 'yan shekarun baya, kasashen Sin da India suna bunkasuwa da sauri, amma mugun tsari na fannoni daban daban ya kayyade su sosai, idan ba a warware matsalolin ba yadda ya kamata, ba za su iya samun ci gaba da sauri a fannin karfin tserereniya dangane da tattalin arziki ba.

Malam Augusto Lopez Claros, babban kwrarren dandalin tattaunawa na duniya a kan tattalin arziki kuma darektan sashen da ke kula da binciken karfin tserereniya na kasashe daban daban na dandalin yana ganin cewa, a 'yan shekarun baya, kasar Sin tana bunkasuwa da sauri a sakamakon manufofinta ta bude kofa ga duniya da yin gyre-gyare a gida. Domin kara karfafa karfin tserereniyarta, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa ingancin bakunanta da kara gina manyan ayyuka da kyautatta tsarin kiwon lafiya da na ba da ilmi.

A cikin ko wace shekara na shekaru 26 da suka gabata, dandalin tattaunawa na duniya a kan tattalin arziki ya bayar da rahoto a kan karfin tserereniya ta kasashe daban daban. Rahoton da ya bayar a shekarar da muke ciki ya shafe kasashe da yankuna da yawansu ya kai 117. An rubuta wannan rahoto ne bisa kididdgar da aka bayar a fili, da kimantawar da dandalin ya yi da kuma amsoshin da shugabannin gwamnatoci da kamfanoni daban daban suka bayar game da tambayoyin da dandalin ya yi musu.(Danladi)