Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-28 14:12:03    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(22/9-28/9)

cri
Ran 24 ga wata, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayar da alama ta 'tsabtattacen wasannin Olympic' na Beijing na shekarar 2008. An zana wani babban itace, wanda jikinsa ya yi kama da wani mutum, wannan zane ya alamta cewa, dan Adam da muhalli suna yin zaman tare cikin jituwa, ya nuna ci gaban muhalli mai dorewa. 'Tsabtattacen wasannin Olympic' yana daya daga cikin manyan manufofi 3 da za a aiwatar a lokacin wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008, ma'anarsa ita ce shirya wasannin Olympic bisa ra'ayoyin kiyaye muhalli da albarkatun kasa da kuma daidaituwar yanayin kasa.

An yi babban taron kamfannonin watsi shirye-shirye na kasa da kasa don wasannin Olympic na Beijing a nan birnin Beijing daga ran 21 zuwa 23 ga wata. Wakilai daga kamfanin NBC na kasar Amurka da kawancen kamfannonin watsa labaru na Turai wato EBU da kawancen kamfannonin watsa labaru na Asiya da yankin Tekun Pasific wato ABU da kuma gidan talibijin na tsakiya na kasar Sin wato CCTV sun halarci wannan taro, wadanda za su watsa shirye-shirye na talibiji a lokacin wasannin Olympic na shekarar 2008. wakilai masu halartar taron sun tattauna ayyukan watsa shirye-shiryen talibiji a lokacin wasannin Olympic da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, a gun wannan babban taro da aka yi a ran 22 ga wata, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Mr. Liu Qi ya yi jawabi cewa, kwamitin nan zai bi al'adun duniya, zai kuma yi koyi da fasahohin da aka samu wajen cin nasarar gudanar da wasannin Olympic a da, zai ba da hidima mai kyau ga kafofin yada labaru da suka watsa labaru kan wasannin Olympic na shekarar 2008, musamman ma zai ba da sauki ga kafofin yada labaru na kasashen waje daga fannoni daban daban.

An kammala budadiyyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin ta shekarar 2005 a ran 25 ga wata. A cikin karo na karshe na gasa ta tsakanin mata biyu biyu da aka yi a ran nan, 'yar wasan kasar Spain Nuria Llagostera Vives da 'yar wasan kasar Venezuela Maria Vennto-Kabchi sun lashe 'yan wasan kasar Sin Zheng Jie da Yan Zi da ci biyu ba ko daya, sun zama zakaru, 'yan wasan kasar Sin sun zama na 2. 'Yar wasan kasar Rasha Maria Kirilenko ta zama zakara a cikin gasar tsakanin mace da mace. An bude wannan budadiyyar gasa a ran 10 ga wata, dan wasan kasar Spain Rafael Nadal ya zama zakara a cikin gasar tsakanin namiji da namiji, dan wasan kasar Amurka Justin Gimelstob da dan wasan Australia Nathan Healey sun zama zakaru a cikin gasa ta tsakanin maza biyu biyu.

An ci gaba da yin gasar fid da gwani ta wasan kwallon kafa ta duniya da Hadadiyyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya ta shirya don matasan da shekarunsu ba su kai 17 da haihuwa ba a kasar Peru. A cikin gasar tsakiya na kusa da na karshe da aka yi a ran 25 ga wata. Kungiyar kasar Turkey ta lashe kungiyar kasar Sin da ci 5 da 1, ta haka kungiyar kasar Sin ba ta shiga karon kusa da karshe ba, amma ta zama kungiyoyi masu gwaninta guda 8. Kungiyar kasar Sin ta taba samun irin wannan maki a cikin gasa ta karo ta farko da aka yi a kasar Sin a shekarar 1985.

An rufe budadiyyar gasar wasan kwallon tebur a birnin Yokohama na kasar Japan a ran 25 ga wata. 'Yar wasan kasar Sin Zhang Yining ta sami lambar zinare a cikin gasar tsakanin mace da mace bayan da ta lashe abokiyarta Guo Yan da ci hudu ba ko daya, haka kuma 'yan wasan kasar Sin Bai Yang da Cao Zhen sun zama zakaru a cikin gasa ta tsakanin mata biyu biyu. Dan wasan kasar Jamsu Timo Boll ya sami lambar zinare a cikin gasar tsakanin namiji da namiji, sa'an nan kuma shi da abokinsa Christian Suss sun zama zakaru a cikin gasa ta tsakanin maza biyu biyu.(Tasallah)