A gun taron yanayin kaka da aka yi a ran 24 ga wata a birnin Washington, hukumar tsai da kudurin kungiyar IMF wato asusun ba da lamuni ta duniya wato kwamitin kudi na kasashen duniya ya yarda da wani shirin soke basussuka wadanda yawansu ya kai dola biliyan 40 da kasashe mafiya talauci na duniya suka ci. Hukumar direktoci ta zartaswa ta kungiyar IMF za ta shirya taro nan gaba kadan don yarda da wannan shiri da gaske.
Da akwai kasashe 18 wadanda suka samu moriya da farko daga wajen wannan shiri, yawancinsu kasashen Afirka ne. Za a soke basussukansu wadanda yawansu ya kai dola biliyan 40 da wadannan kasashe suka ci daga wajen kungiyar IMF da bankin duniya da sauran hukumomin kasashen duniya. Ban da wannan kuma da akwai sauran kasashe 20 wandada za a rage ko kuma soke basussukan da suka ci bisa sharuda. Da haka ne, jimlar basussukan da za a soke ta wuce dala biliyan 55. A gun taron manema labaru da aka shirya, Gordon Brown, shugaban kwamitin kudi na kasashen duniya, kuma ministan kudi na Ingila ya bayyana cewa, bisa kokarin da aka yi cikin 'yan watannin da suka wuce, wakilai masu yin shawarwari sun daddale yarjejeniya kan abubuwan da aka tattauna cikin wannan shiri.
Wannan shirin soke basussuka wanda aka tsai da shi bisa alkawarin da shugaban rukunin kasashe 8 wato Amirka da Jamus da Japan da Ingila da Canada da Faransa da Italiya da Rasha suka dauka a gun taron da suka yi a watan Yuli na wannan shekara a kasar Scotland. A lokacin rukunin kasashen 8 ya ba da shawarar soke basussukan da kasashe mafiya talauci suka ci daga wajen kungiyar IMF da bankin duniya da bankin raya Afirka. Ko da yake kungiyar IMF ta yarda da ra'ayin soke ikon mai ba da bashi ga kasashe masu talauci, amma wajibi ne za a yi shawarwari a tsakaninta da bankin duniya kan wannan matsala, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da akwai wasu jami'an bankin duniya da wasu kasashe wadanda suka nuna kiyewa ga wannan shirin soke basussuka. Sun bayyana cewa, soke basussuka da yawa zai dakushe karfin bankin duniya wajen hada-hadar kudi da ba da bashi. Idan da ba a shawo kan masu yin kiyayya da samun goyon baya daga wajen su ba, hukumar direktocin bankin duniya ba za ta iya samun isasshen kuri'u domin zartas da wannan babban shirin rage basussuka ba.
Domin shawo kan masu nuna kiyewa ga bankin duniya da su goyi bayan shirin soke basussukan kasashe masu talauci, cikin wasikar da ministocin kudi na rukunin kasashe 8 suka rubuta wa Paul Wolfovitz sun bayyana cewa, rukunin zai dauki nauyin duk hasarar da bankin duniya zai samu sabo da rage basussuka.
An labarta cewa, bankin duniya da hukumar direktoci ta zartaswa ta kungiyar IMF sun yarda da wannan shiri da sauri, kuma za a fara aikawatar da shirin kafin karshen wannan shekara. Manazartan tattalin arziki sun bayyana cewa, ko da yake soke basussukan kasashe masu talauci ya dan sassauta wahalolin da wadannan kasashe ke sha wajen tattalin arziki, wadannan kasashe kuma za su nuna babban goyon bayansu ga aikin tabbatar da manufar samun bunkasuwa ta shekaru dubu daya, amma wannan ba zai iya kawar da talaucinsu kwata-kwata ba.
Kasashen Afirka suna maraba da wannan shirin soke basussuka, sa'an nan kuma sun bayyana cewa, ya kamata a soke basussukan da kasashe masu talauci suke ci ba tare da kowane sharadin siyasa ba. Im da ba haka ba, wannan shiri zai zama wata takarda ce kawai. (Umaru)
|