Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na duniya ina labari na yau: Babbar madatsar ruwa mai suna Zipingpu na lardin Sichuan wannan shi ne babban aiki daya daga cikin manyan ayyukan gine gine guda l0 na raya wuraren dake yammacin kasar Sin, Tun daga shekara ta 2001,an fara yin gine ginen nan, jimlar kudaden da aka zuba ga wannan babban aiki sun kai kudin Sin yuan biliyan 6.97, kuma tsawon lokacin gine ginen nan sun kai shekaru 6.
A cikin gine ginen babban aikin, ma'aikata sun gamu da wahalhalu, sabo da manyan tuddai dake ciki, kuma a kan wutsiyar kogin akwai wata babbar madatsar ruwa wadda ta shahara a duk kasar Sin mai suna Dujiangyan, yawan fadin gonaki da jimlar mutane dake shan ruwa daga wannan babbar madatsar ruwa DuJianyan sun kai kashi daya cikin hudu bisa na duk lardin Sichuan, kuma jimlar kudaden da aka samu daga wannan babbar madatsar ruwa sun kai kashi 60 cikin dari da kashi 50 cikin dari bisa na jimlar kudaden da duk wannan lardin ya samu. Sabo da labarin kasa yana da wahalhalu wajen ginawa, ta haka ne gine gine na wannan babbar madatsar ruwa da ingancin tafiyar da ruwa dukkansu sun gamu da babbar wahala, Ban da haka kuma, domin yawan ruwan dake cikin wannan madatsar ruwa sun yi yawa sosai, sai ya kamata a yi la'akari kan yadda in wannan babbar madatsar ruwa ta lalace sai mai yiyuwa ne in wannan babbar madatsar ruwa za ta rushe har za ta kawo masifa ga mutanen dake kan karkarar shiyya dake karkashin wannan babbar madatsar tuwa.
Duk domin yin gine gine wannan babban aiki da kyau da kulawa da shi da kyau, tun daga farko ne an fara tattara masu kimiyya da kwararru har da gayyaci wadansu shahararrun kwararru na duk duniya don yin bincike da tattaunawa abubuwan da za a gamu da su cikin wannan babban gine gine, ban da haka kuma a yi cudanya da wannan babban aiki tare da kasuwannin tattalin arziki don neman kara samu bunkasuwar tattalin arziki sosai. Ta hanyoyin zamani ne a gano sabuwar fasaha kan gine ginen nan, kuma an haye wahalhalu da yawa da cikin duk tsawon gine gine, domin wannan babban aiki wato babbar madatsar ruwa za ta ci jarabawa daga zuri'a zuwa zuri'a.
Amma,yanzu an kusan kammala wannan babban aiki,Tsayin wannan babbar madatsar ruwa daga sama ya kai mita 880, bisa shirin da aka tsara, karshen watan Satumba na shekarar nan da muke ciki, wannan babbar madatsar ruwa za ta fara jawo ruwa, kuma a waton October na wannan shekara za a fara hauda jananeta.
Ban da wannnan babbar madatsar ruwa mai suna Zipingpu ga wata babbar madatsar ruwa mai suna Dujiangyan wadda ta shahara a duk duniya, yanzu fadin gonakin da suke shan ruwan wannan babbar madatsar ruwa sun kai kadada l009, kuma jimlar hatsin da akan samu a kowce shekara daga wannan karkarar dake kusa da babbar madatsar ruwa sun kai kilo biliyan 6,ban da haka kuma wannan babbar madatsar ruwa ta samar da ruwa ga mutane na birane manya da na matsakaita guda 50 da masana'antu fiye da daruruka na lardin Sichuan.
Bayan da za a kammala wannan babbar madatsar ruwa mai suna Zipingpu, yawan ruwan da wannan babbar madatsar ruwa za ta dauka za su kai cubic mita biliyan l.ll, Kuma za ta samar da ruwa ga mutane na birane manya da na kanana fiye da dari da shayar da gonakai masu yawa sosai da sosai.(Dije)
|