A kwanan baya, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gabatar da "manufar cinikin motoci" don kara kyautata tsarin kula da harkokin cinikin motoci. Kwararru sun nuna cewa, za a ci gajiyar manufar nan sosai wajen kafa kyakkyawan tsarin kasuwannin sayar da motoci, da kare moriyar masu sayen motoci, da gaggauta bunkasa masana'antun kera motoci a kasar Sin.
Bisa ci gaba da ake samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da kyautata matsayin zaman rayuwar jama'a, yanzu kasar Sin ta riga ta zama wata babbar kasa da ake sarrafa motoci, da sayensu. Yawan motoci da aka sarrafa a kasar Sin tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuli na shekarar nan ya kai miliyan 3 da dubu 30, wato ke nan ya karu da kashi 23 cikin dari bisa na makaman lokaci na bara, haka nan kuma yawan motoci da aka sayar a kasar Sin shi ma ya kai miliyan 2 da dubu 900, wato ke nan ya karu da kashi 20 cikin dari bisa na makamacin lokaci na shekarar bara.
Da Malam Zhang Xiaoyu, mataimakin shugaban kungiyar hadin giwar masana'antun kera injuna ta kasar Sin ya tabo magana a kan wannan manufar, sai ya bayyana cewa, "za a sami taimako sosai daga wajen wannan manufar don bunkasa masana'antun sarrafa motoci na kasar Sin. Makasudin manufar nan shi ne domin cika alkawarin da muka dauka yayin da aka shigar da kasar Sin cikin kungiyar cinikin duniya wato WTO. Wato za a bude wa kasashen waje kasuwannin sayar da motoci na kasar Sin. Haka zalika manufar nan za ta taka muhimmiyar rawa wajen kara daga matsayin kasar Sin cikin takarar da ake yi a kasuwannin sayar da motoci don kara biya wa masu sayen motoci bukatunsu."
Bayan haka Malam Zhang Xiaoyu yana ganin cewa, wani makasudi daban na wannan manufa da gwamnatin Sin ta bayar shi ne domin neman kafa kyakkyawan tsarin kasuwannin sayar da motoci bai daya da kuma bude wa kasashen waje kofa. Manufar nan ta bayyana a fili cewa, kasar Sin za ta kafa tsarin kasuwannin sayar da motoci da zai tashi daidai da na duniya.
Daga manufar nan, ana iya gano cewa, kafa kyakkyawan tsarin kasuwannin sayar da motoci da kare iko da moriyar masu sayen motoci manyan abubuwa biyu ne da aka tanada a cikin manufar. Manufar ta nuna cewa, tun daga ran 1 ga watan Disamba na shekarar 2006, duk motoci da za a sayar a kasar Sin za su kasance dauke da sunayensu da kuma bayanoninsu, sa'an nan kuma wajibi ne a yi wa motocin sabis. Haka zalika manufar ta tanada a fili cewa, wajibi ne, 'yan kasuwa masu sayar da motoci su samar da kayayyakin sauyi iri-iri na motocin da suka sayar.
Haka kuma ko motoci da aka daina kera su ma, ya kamata, 'yan kasuwan su yi kokarin daukar matakai wajen samar da kayayyakin sauyinsu a cikin kyayadadden lokaci da aka tsai da.
A ganin shehu malami Han Meng wanda ke aiki a ofishin tattalin arziki na cibiyar nazarin al'amuran yau da kullum ta kasar Sin, wani abu cikin wannan manufar da ke jawo hankulan mutane shi ne an sassauta kasuwannin sayar da motocin kunce. Ya ce, "abubuwa da aka tanada cikin manufar nan dangane da sassauta kasuwannin sayar da motocin kunce sun jawo hankulan bangarori daban daban. An kyautata zaton cewa, yawan motocin kunce da za a sayar a kasuwanni a nan gaba ba da dadewa ba zai wuce sabbin motoci da za a sayar. Sabo da motocin kunce da ake sayarwa suna karuwa, za a gaggauta bunkasa harkokin hayar motoci da gwanjonsu da kayatar da su da kuma sauransu, ta haka kuma za a gaggauta bunkasa masana'antun kera motoci daga fannoni daban daban. (Halilu)
|