Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-22 17:35:19    
Jin Yongjian ya yi fatan za a tabbatar da matsayi da amfani na Majalisar cikin himma da kwazo a bayyane

cri
Kwanan baya, a babbar hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, an yi taron shugabanni na tunawa da ranar cika shekaru 60 da kafa Majalisar, shugabannin kasashe da na gwamnatoci fiye da 150 sun yi shawarwari a fannoni da yawa na yin gyare-gyare kan Majalisar da bunkasuwar duniya da tsaron kai cikin tarayya da sauran batutuwa, kuma sun zartas da wata takardar sakamako da ke kunshe da abubuwan gyare-gyare kan fannoni da yawa. Tsohon mataimakin babban sakataren Majalisar kuma shugaban hadadiyyar kungiyar kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Jin Yongjian ya karbi ziyarar da manema labaru suka yi masa, inda ya yi fatan za a tabbatar da matsayi da amfani na Majalisar cikin himma da kwazo a bayyane ta hanyar taron shugabanni da sauran aikace-aikace.

Majalisar Dinkin Duniya kungiya ce ta gwamnati da gwamnati da ke da halin wakiltar kowa da kowa a ko'ina tare da ikon fada a ji, kuma ba za a yin biris da taimakonta wajen harkokin kasa da kasa ba. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ikonta na fada a ji na ta shan kalubale, har ana shakkar matsayinta da amfaninta. Mr Jin Yongjian yana ganin cewa, akwai wajabcin sake tabbatar da matsayi da amfani na Majalisar ta hanyar aikace-aikacen tunawa da ranar cika shekaru 60 da kafa ta. Ya bayyana cewa, a cikin amfanin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, muhimmin aiki shi ne tsara ka'idoji da dokokin kasashen duniya da yarjejeniyoyi iri daban daban na tsakanin kasa da kasa. Ina fatan za a iya tabbatar da matsayi da amfani na Majalisar Dinkin Duniya cikin himma da kwazo a bayyane.

Lokacin da Mr Jin Yongjian ya karbi ziyarar, Ya yi magana kan batun gyare-gyaren Majalisar Dinkin Duniya wanda ke jawo hankulan mutane sosai. Ya bayyana cewa, in an kwatanta farkon kafuwarta, Majalisar ta sami manyan sauye-sauye a halin yanzu na fuskantar al'amuran kasashen duniya da kuma mambobin da ke cikinta da dawainiyar tarihi da ke bisa wuyanta da saruan fannoni. Don biyan bukatun sabuwar dawaniya a sabon halin da ake ciki , dole ne a yi gyare-gyare kan Majalisar Dinkin Duniya, wannan ya riga ya zama ra'ayi daya da kasashe mambobi daban daban na Majalisar suka samu. Mr Jin Yongjian ya karfafa cewa, ya kamata a yi gyare-gyare kan Majalisar daga dukkan fannoni. Ya ce, gayre-gyaren da za a yi kan Majalisar Dinkin duniya gyare-gyare ne da za a yi a dukkan fannoni ,dimbin kasashe masu tasowa ba su mai da hankali sosai ga gyare-gyaren da za a yi kan kwamitin sulhu ba, suna fatan Majalisar za ta iya gaggauta gamayyar kasa da kasa da su aiwatar da wasu hakikanan ayyuka da kuma daukar hakikanin mataki wajen batun raya kasa da kawar da talauci da maganin cutar sida da sauran irin makamatansu,, amma ba sake maimaita alkawarin da suka taba yi a da kawai ba.

Mr Jin Yongjian ya bayyana cewa, ya yi fatan Majalisar Dinkin Duniya za ta iya bayyana da kuma kiyaye moriyar dimbin kasashe masu tasowa bisa sharadin kula da moriyar bangarori daban daban wajen yin gyare-gyare don sa kaimi ga ciyar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gaba da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma tabbatar da hakkin dan Adam da ciyar da shi gaba, har ma ta kara ba da gudumuwa mai amfani wajen tsara ka'idojin kasa da kasa ta yadda za ta zama wata hukuma mai kwarjini tare da samun sakamakon aiki da yawa.

Game da gyare-gyaren da za a yi kan Majalisar, Mr Jin Yongjian ya bayyana cewa, dayake kasashe mambobin da ke cikin Majalisar suna samun babban sabani a tsakaninsu kan batun yin gyare-gyare kan kwamitin sulhu, ba za a iya daidaita batun ba sai ta hanyar yin shawarwari a fannoni daban daban cikin hakuri da juna, kuma kayyadadden lokacin yin gyare-gyare kan kwamitin sulhu ba abun wayar da kai ba, kuma ba dace da halin yanzu da ake ciki ba. Ya ce, gyare-gyaren da za a yi kan kwamitin sulhu ya shafi bambancin matsayi da moriya da ke kasancewa a tsakanin kasashe mambobin da ke cikin Majalisar, bisa halin da ake ciki na kasancewar babban sabani, aikin gaskiya da za a yi shi ne, kara neman ra'ayi daya a bangarori mafi yawa ta hanyar yin shawarwari sosai kuma cikin hakuri da juna, amma ba tilasta a jefa kuri'a da kuma kayyade lokaci ba.(Halima)