Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-20 15:40:30    
Ziyarar Hu Jintao a kasashen waje ta sami sakamako da yawa

cri
Daga ran 8 zuwa ran 17 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyarar aiki a kasar Canada da Mexico, kuma ya halarci taron shugabanni na murnar ranar cika shekaru 60 da kafa Majalisar Dinkin Duniya, sa'anan kuma ya yi aikace-aikacen diplomasiya har sau 50 ko fiye, kuma ya sami sakamako da yawa. Kafin kammala ziyarar, ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya bayyana wa manema labaru da suka rufa musu baya a gun ziyarar sakamakon da aka samu a gun ziyarar.

Mr Li Zhaoxing ya bayyana cewa, daya daga cikin sakamakon da aka samu a gun ziyarar shi ne kara ciyar da dangantakar sada zumunta da hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasar Canada da Mexico gaba daya a dukan fannoni gaba.

A shekarar 1997, kasar Sin da kasar Canada sun kulla huldar abokantaka a dukan fannoni. A duk tsawon lokacin ziyarar, gaba daya ne Mr Hu Jintao da firayim ministan kasar Canada Paul Martin suka tsai da kudurin kara daga huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Canada zuwa matsayin huldar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare da kuma sa kaimi ga hadin guiwar da ke tsakanin kasashen biyu daga dukan fannoni tare da bangarori da yawa da kuma tabbatar da manufar hakika. Bangarorin biyu sun kuma daddale yarjejeniyoyin hadin guiwa guda 7 da suka shafi zirga-zirgar jiragen sama da jiragen kasa da makamashin nukiliya da sauran fannoni.

Kasar Sin da kasar Maxico dukansu suna cikin jerin manyan kasashe masu tasowa, kuma suna fuskantar dawaniyar raya kasa iri daya, kara zurfafa hadin guiwar da ke tsakanin bangarori biyu shi ne batu mai muhimmanci ga shawarwarin da ke tsakanin shugabannin kasashen biyu. gaba daya ne bangarorin biyu sun yarda da daukar hakikanin mataki don kara zurfafa huldar abokantaka da ke tsakanin kasar Sin da kasar Mexico bisa manyan tsare-tsare , kuma za su tsara shirin aiki na gaba dayansu ba tare da bata lokaci ba.

Taron shugabanni na murnar ranar cika shekaru 60 da kafa Majalisar Dinkin Duniya shi ne taron da aka kira bisa mataki mafi girma a tarihin Majalisr Dinkin Duniya, shugabannin kasashe da na gwamantoci da ke cikin Majalisar da yawansu ya kai 170 sun halarci taron. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarci taruruka sau da yawa, kuma ya bayar da jawabai masu muhimmanci. A gun cikakken taron, shugaba Hu Jintao ya gabatar da ra'ayoyin samun bangarori da yawa da yin hadin guiwar samun moriyar juna da yin hakuri da juna da cim ma buri na samun kwanciyar hankali gaba daya da wadatuwa gaba yada da kafa duniya mai jituwa bisa babban batu na kafa duniya mai zaman lafiya har abada da samun wadatuwa da jituwa gaba daya. Sa'anan kuma Mr Hu Jintao ya gabatar da matsayin kasar Sin na nuna tsayayyen goyon baya ga ra'ayin kasashe masu tasowa mai adalci, kuma ya kirayi Majalisar Dinkin duniya da ta kara ba da gudumuwarta wajen samun bunkasuwa, sa'anan kuma ya yi shelar manyan matakan da kasar Sin ta dauka wajen buga harajin kwastan da harkokin basusuka da ba da rancen kudi bisa gatanci da kiwon lafiyar jama'a da raya albarkatan karfin dan adam da sauran fannoni da kuma nuna goyon baya ga sauran kasashe mau tasowa wajen kara samun bunkasuwa da sauri . Mr Hu Jintao ya kuma karfafa cewa, ba za a iya maye gurbin kwamitin sulhu ba wajen ba da taimako ga daidaita batutuwan da suka shafi tsaron kai da zaman lafiya na duniya , ya kamata a ba da tabbaci ga kwamitin sulhu wajen aiwatar da hakkin da babban tsarin Majalisar dinkin Duniya ke dora masa da kuma kiyaye kwarjinin kwamitin da kara karfinsa na samun sakamakon aiki, ya kamata kwamitin sulhu ya lura da batutuwan da suka jawo hankulan kasashen Afrika da kara zuba jari a ciki. Mr Hu Jintao ya kuma sake jaddada goyon bayan da kasar Sin take nunawa ga yin gyare-gyare kan Majalisar Dinkin Duniya, kuma ya hakakke cewa, ya kamata a yi gyare-gyare kan manyan fannoni da kuma aiwatar da dimokuradicya da yin shawarwari a tsakanin bangarori da yawa.

Wadannan ra'ayoyi sun sami maraba sosai daga wajen shugabannin kasashe daban daban, musamman ma daga shugabannin kasashe masu tasowa da gamayyar kasa da kasa.

Ziyarar Hu Jintao ta sa gamayyar kasa da kasa ta kara fahimtar manyan tsare-tsaren kasar Sin na raya kasa cikin lumana .(Halima)