Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-19 16:59:16    
Hu Jintao ya yi muhimmin jawabi a gun taron shugabanni na tunawa da ranar cika shekaru 60 da aka kafa MDD

cri

A ran 15 ga watan nan an yi cikakken zama na biyu na taron shugabanni na tunawa da ranar cika shekaru 60 da aka kafa MDD. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya halarci taron kuma ya bayar da muhimmin jawabi mai suna "A yi kokarin kafa duniya mai jituwa ta zaman lafiya mai dorewa da wadata tare", inda ya bayyana ra'ayi da matsayi na kasar Sin kan halin da a ke ciki a duniya da muhimman maganganun kasashen duniya, kuma ya gabatar da hakikanin ra'ayi a wajen karfafa amfanin MDD da sa kaimi ga gyare gyaren MDD da sa kaimi ga gama kan kasashen duniya na raya kasa. Yanzu sai ku saurari labarin da aka ruwaito mana.

Goran Persson, firayim ministan kasar Sweden kuma shugaban babban taro na 60 na MDD da Omar Bango, shugaban kasar Gabon kuma shugaban babban taro na 59 na MDD sun gama kai don shugabantar cikakken zama na biyu na taron shugabanni na tunawa da ranar cika shekaru 60 da aka kafa MDD, shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatocin da ke halartar taron sun ci gaba da yin tattaunawa kan maganar gyare gyaren MDD da kiyaye zaman lafiyar duniya da ingiza gama kai don raya kasa.

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi jawabi a gun taron, inda ya nuna cewa, kafuwar MDD wani babban al'amari ne mai muhimmancin gaske a kan tarihin Dan Adam. A shekaru 60 da suka shige MDD ta ba da muhimmin amfani a wajen kiyaye zaman lafiya da samun ci gaba tare da yalwata wayin kai na 'yan Adam, kuma ta samu babbar nasara. Ya ce, Da ya ke MDD cibiya ce ta tsarin kiyaye zaman lafiyar tarayya, dole ne a karfafa amfaninta, amma ba dakushe ta ba. Ya kamata mu kafa sabon ra'ayin zaman lafiya na amincewa juna da moriyar juna da daidaici da gama kai don mu kafa tsarin zaman lafiyar tarayya mai amfani, ya kamata mu nuna goyon baya ga daidaita hargitsin kasashen duniya cikin lumana, ya kamata mu karfafa gama kai, mu tsaya tsayin daka mu kai naushi ga ta'addanci.

Hu Jintao ya ce, Ya kamata MDD ta dauki hakikanin mataki don aiwatar da takitin raya kasa na shekaru dubu, musamman ta yi kokari a wajen ingiza kasashe masu tasowa su kara hanzari a wajen raya kasa don a sa karni na 21 ya zama karnin da kowa ya iya more ci gaba.

A shekaru 60 da aka kafa MDD, ta ba da amfani mai muhimmancin gaske a wajen kiyaye zaman lafiyar duniya da sa kaimi a wajen samun ci gaba tare. Yanzu al'amuran kasashen duniya sun yi manyan sauye sauye. Kasar Sin tana nuna goyon baya ga gyara MDD. Hu Jintao ya ce, Ya kamata a gyara MDD daga duk fannoni. A wajen gyara kwamitin sulhu ya kamata a kara wakilcin kasashe masu tasowa, musamman na kasashen Afrika don kasashe madaidaita da kanana su kara samun damar halartar aikin tsai da manufa na kwamitin sulhu. (Dogonyaro)