Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-15 18:26:15    
An yi taron dandalin fadi albarkatun bakinka kan harkokin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan

cri

A ran 15 ga wata wato ranar Alhamis a birnin Shanghai, an fara taron dandalin fadin albarkatun bakinka kan harkokin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Mr. Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da Mr. James CY Soong, shugaban jam'iyyar the People First Party ta Taiwan sun halarci bikin kaddamar da taron, kuma sun bayar da jawabai bi da bi.

A gun taron, Mr. Jia Qinglin ya bayar da wasu ra'ayoyi kan yadda za a zurfafa da kara yin mu'amala da hadin guiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin gabobin 2. Sannan kuma Mr. James Soong ya ce, idan dangantakar da ke kasancewa a tsakanin gabobi 2 ba ta cikin hali mai dorewa, to ba shakka tattalin arzikin Taiwan ba zai samu ci gaba mai dorewa ba. Don haka, ya kamata a kafa tsarin amincewa da juna a tsakanin gabobin 2 a fannin tattalin arziki. (Sanusi Chen)