Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-15 17:23:08    
Abbas yana shirin rushe kungiyoyin dakaru daban daban na Palasdinu

cri

A 'yan kwanakin nan, Rafiq Husseini, darektan ofishin kula da harkokin shugaban hukumar Palasdinu Mahmoud Abbas ya bayyana cewa, hukumar Palasdinu tana shirin bukatar kungiyoyin dakaru daban daban na Palasdinu da su kwance damara bayan da aka kawo karshen zaben kwamitin kafa dokoki na Palasdinu a watan Janairu na shekara mai zuwa. To, wannan ya bayyana cewa, Abbas ya fara daukar matakai wajen daidaita matsalar kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi bayan da Isra'ila ta janye jikinta daga zirin Gaza, da nufin tabbatar da zaman lafiyar siyasa da sake yin shawarwari da Isra'ila cikin lumana.

Malam Husseini ya ce, da farko, hukumar za ta rushe kungiyoyin dakaru a karkashin shugabancin babbar kungiyar dakaru wato Kungiyar 'yantar da al'ummar Palesdinu wato Fatah, domin nuna niyyar hukumar da sahihiyar zuciyarta. Bayan haka, za ta dauki matakai ga kungiyar Hamas da dai sauran kungiyoyin dakaru. Malam Husseini ya ci gaba da cewa, daga makon gobe, za a mayar da dukkan dakaru dubbai a karkashin kungiyar Fatah da su zama sojojin kiyaye zaman lafiya na Palasdinu. Bayan an kammala zaben kwamitin kafa dokoki na Palasdinu, wannan aikin rushe kungiyoyin dakaru zai shiga cikin karshen wa'adi. A wancan lokaci, Malam Abbas zai bukaci kungiyoyin dakarun da suke kan kujerun kwamitin kafa dokoki da su rushe dakarunsu da kansu.


1  2  3