Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-15 10:38:38    
Kasashen da suka zuba jari a Afrika ba su samu sakamako mai kyau ba

cri

A ran 13 ga watan nan a Geneva taron ciniki da raya kasa na MDD ya bayar da Rahoto kan ci gaban tattalin arziki na Afrika na shekara ta 2005, inda ya nuna cewa, a shekarun baya kasashen waje sun kara zuba jari ga Afrika, amma ba su samu sakamako mai kyau ba.

Rahoton nan ya nuna cewa, a shekara ta 1980 yawan jarin da kasashen waje suka zuba wa Afrika kai tsaye shi ne dollar biliyan 2.2, a shekara ta 1990 ya karu zuwa dollar biliyan 6.2, a shekara ta 2003 shi ne dollar 13.8. a shekara ta 2004 ya kai dollar biliyan 18.

Amma a ganin rahoton nan, in an kwatanta yawan jarin da a ke zubawa a duk fadin duniya, jarin da aka zuba wa Afrika ya yi kadan.

Rahoton nan ya bayyana cewa, kasashen duniya suna zuba jari ga wasu kasashen Afrika kawai. Bias lissafin da aka yi an ce, jarin da kasashen waje suka zuba a kasashe 10 wato Morocco da Equatoril Guinea da Angola da Sudan da Nigeria da Chad da Afrika ta kudu da Libia da Algeria da Tunisia ya tashi kashi 3 cikin kashi 4 in an kwatanta shi da na jimlar jarin da kasashen waje suka zuba wa Afrika. Kuma ana zuba jari ne musamman ga sana'ar ma'adinai da murdo man fetur. A cikin shekaru 10 wato daga shekara ta 1988 zuwa shekara ta 1997, yawan jarin da kasashen waje suka zuba wa sana'o'in sarrafa danyun kayayyaki na Afrika ya karu daga kashi 51.8 cikin kashi 100 zuwa kashi 53.4 cikin kashi 100, amma a tsawon lokacin nan, yawan jarin da kasashen waje suka zuba wa wadannan sana'o'I a kasashen Asia da kasashen Latin Amurka ya ragu daga kashi 8.8 cikin kashi 100 zuwa kashi 3.5 cikin kashi 100 da kashi 5.7 cikin kashi 100. sabo da haka irin wannan hanyar zuba jari ga kasashen Afrika ba ta yi amfani yadda ya kamata a wajen bunkasa tattalin arziki na Afrika ba.

Rahoton nan ya nuna cewa, ban da haka kuma akwai dalilin tarihi da ya sa aka bi hanyar da a ke samun jari a halin yanzu, wato kasashen Afrika suna dogara da wasu kasashe kawai. A cikin shekaru 20 wato daga shekara ta 1980 zuwa shekara ta 2000, jarin da aka samu daga Faransa da Ingila da Amurka ya kai kashi 70 cikin kashi 100 na adadin jarin da kasashen Afrika suka samu daga kasashen waje.

Rahoton nan ya bayyana cewa, ko da ya ke kasashen Afrika sun yi babban kokari, amma a shekaru 20 da suka shige duk Afrika ba ta samu ci gaba a bayyane a wajen bunkasa tattalin arziki da zaman tarayya ba. Daya daga cikinn dalilan da suka sa Afrika ta yi haka shi ne matsalar jarin da kasashen waje ke zubawa a Afrika.. A ganin rahoton nan, ya kamata kasashen duniya su yi tunani kan yadda za a yada amfanin jarin da kasashen waje suka zuba. A ganin rahoton nan, dole ne masu zuba jari na kasashen waje su yi la'akari da halin da a ke ciki a Afrika da matsalolin da kasashen Afrika suka gamu da su a wajen bunkasa tattalin arziki. Mahukuntan kasashen Afrika ma ya kamata su tsamo fasahohi masu amfani daga kasashen Asia, su dauki jarin waje a kama da wani muhimmin kashi a wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, kuma su kago muhalli mai kyau ga kasashen waje da za su zuba jari don samu ci gaba mai dorewa. (Dogonyaro)