Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-14 17:50:20    
Yawan makamashin da kasar Sin ke iya cin gashin kanta ya kai kashin 94 bisa 100

cri
A gun taron manema labaru da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 13 ga wata, Mr. Zhang Guobao, mataimakin direktan kwamitin bunkasa da yin gyare- gyaren kasar Sin ya bayyana cewa, manufar bunkasa makamashi ta kasar Sin ta tsaya kan matsayin kasar, yanzu yawan makamashin da kasar Sin ke iya cin gashin kanta ya kai kashi 94 bisa 100, yawan makamashin da take dogara bisa kasashen waje ya kai kashi 6 bisa 100 kawai. Sa'an nan kuma ya bayyana cewa, bunkasuwar da kasar Sin ta samu wajen tattalin arziki da makamashi ta kawo babban zarafin kasuwanci ga duniya, nan gaba kasar Sin za ta kara hadin gwiwa da kasashe daban-daban na duniya wajen makamashi. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayani game da wannan bayani.

Tun daga shekarar 2004 zuwa yanzu, farashin gurbtaccen man fetur na kasashen duniya ya yi ta hauhawa, sabo da haka matsalar makamashi ta zama wata muhimmiyar matsala da ta jawo hankulan kasashen duniya gaba daya. dalilin hauhawar gurbtaccen man fetur, wasu mutanen kasashen waje sun bayyana cewa, dalilin da ya sa hauhawar gurbtaccen man fetur shi ne sabo da yawan gurbtaccen man fetur da ake bukata a kasar Sin da Indiya da sauran kasashe masu tasowa ya karu. A gun taron manema labaru da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a yau, Mr. Zhang Guobao, mataimakin direktan kwamitin bunkasa da yin gyare-gyaren kasar Sin ya bayyana cewa, irin wannan ra'ayi bai bayyana halin da ake ciki a kasuwar makamashin kasashen duniya da gaske ba. "Kasar Sin wata kasa ce mai tasowa, muhimmiyar ka'idar da take bi wajen bunkasa makamashi ita ce ta hanyar tsayawa cikin kasar. Yawan makamashin da take bukata ta hanyar dogara bisa kasashen waje kadan ne. Yawan makamashin da kasar Sin ke iya biyan bukatar kanta ya kai kashi 94 bisa 100, yawan makamashin da take dogara bisa kasashen waje ya kai kashi 6 bisa 100 kawai. "

Domin samun tabbacin samar da makamashim kasar Sin ta riga ta tsai da shirin bunkasa makamashi na matsakaici da dogon wa'adi. Zhang Guobao, mataimakin direktan kwamitin bunkasa da yin gyare-gyaren kasar Sin ya bayyana cewa, "A cikin wannan shiri, an mai da aikin yin tsimin makamashi da daga karfin aiwatar da makamashi bisa matsayi na farko wajen daidaita matsalar makamashi."

Mr. Zhang Guobao, mataimakin direktan kwamitin bunkasa da yin gyare-gyaren kasar Sin ya jaddada cewa, a lokacin da kasar Sin take warware matsalar makamashi ta hanyar tsayawa cikin kasar, kuma tana kara yin mu'amala da hadin gwiwa tare da da sauran kasashen duniya. "Yayin da kasashe daban-daban na duniya suke warware matsalar makamashi, dukkansu sun yi aiki bisa halin da ake ciki a kasashensu a fannin makamashi, kuma suna yin hadin gwiwa da sauran kasashe, wannan ba abun mamaki ba ne. Nan gaba kuma kasar Sin za ta ci gaba da tafiyar da manufar bude kofa ga kasashen waje wajen bunkasa makamashi da samun tabbacin kwanciyar hankali na makamashi, tana son yin shawarwari da hadin gwiwa a tsakaninta da kasashe daban-daban na duniya da kungiyoyin kasashen duniya da manyan kamfanonin da ke tsakanin kasa da kasa a fannin makamashi". (Umaru)