A ran 8 ga wata, mahalartan taron kasa da kasa na 22 kan dokoki sun yi kaura daga birnin Beijing zuwa birnin Shanghai don ci gaba da yin taronsu. Malam Xiao Yang, shugaban babbar kotun jama'a ta kasar Sin kuma babban alkali na farko na kasar ya yi jawabi a gun taron da aka yi a wannan rana, inda ya bayyana wa manyan alkalai na farko da manyan alkalai na kasashe da shiyyoyi sama da 60 wasu abubuwa a kan tsarin dokokin kasar Sin da kuma yadda ake gudanar da dokoki da dai sauransu. Malam Xiao Yang ya ce, yanzu an riga an sami sakamako mai kyau wajen kafa tsarin dokokin kasar Sin. Manufarmu kuma ita ce kafa cikakken tsarin dokoki mai kyau a shekarar 2010.
A cikin shekaru 30 da suka wuce bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, ba a kafa cikakken tsarin dokoki kan harkokin siyasa da na tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a ba. Ya zuwa karshe shekarun 1970, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa, sa'an nan kuma an fara yin kokari sosai wajen kafa tsarin dokoki daga fannoni daban daban. A sama da shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin ta tsara sabon tsarin mulkinta da dokoki sama da 400 da ka'idojin gudanar da harkokin mulki sama da 800, haka nan kuma an yi ta kara kyautata hukumomin dokoki da tsarin dokoki, ta haka an aza harsashi mai kyau ga bin dokoki.
A cikin jawabinsa, malam Xiao Yang ya ce, "bisa ci gaba da ake samu wajen kafa tsarin tattalin arziki na kasuwanni sannu a hankali, musamman ma bayan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO, kasar Sin ta kafa dokoki masu dimbin yawa don dacewa da bunkasuwar tattalin arziki irin na kasuwanni, kuma ta yi canje-canje sosai a kan dokoki dangane da kudin jari da 'yan kasuwa na kasashen waje ke zubawa da ikon mallakar ilmi da dai sauransu, ta yadda dokokin kasar Sin suka dace da ka'idojojin kungiyar WTO, kuma an ba da tabbaci sosai ga hadin guiwa da takarar da kasar Sin ke yi a fannin tattalin arzikin duniya."
Da Malam Xiao Yang ya tabo magana a kan manufar kasar Sin, sai ya ce, kasar Sin za ta kafa cikakken tsarin dokoki mai kyau a shekarar 2010 wadanda suka hada da dokar kasuwancin jama'a da dokar harkokin mulki, da dokar tattalin arziki da dokar kai kara da dokar yanke hukunci kan laifuffuka da dai sauransu. Ya ce, "dokar kasuwanci ta jama'a wata doka ce game da harkokin tattalin arziki na kasuwanni. Dokar tattalin arziki doka ce da ake bi wajen kare tsarin tattalin arziki na kasuwanni ta hanyar sa hannu da gwamnati ke yi cikin harkokin tattalin arziki yadda ya kamata. Haka nan kuma yanzu kasar Sin tana kokari sosai wajen kafa dokar yakar kane-kane da ta kin sayar da kayayyaki masu dimbin yawa da araha da ta ba da rangwamen kudi da sauransu don kara kyautata tsarin dokoki na kasar. "
Bayan haka Malam Xiao Yang ya jaddada cewa, dokar da aka tanada a cikin tsarin mulkin kasar Sin a kan cewa duk mutane su kasance daidai a gaban dokoki, ta nuna babbar niyyar da kasar Sin ta yi don gudanar da harkokin mulki ta hanyar dokoki. Ya ce, " duk mutane su kasance daidai a gaban dokoki, wannan wata doka ce da ta sami amincewa daga wajen kasashe daban daban. A cikin tsarin mulkin kasar Sin an rubuta a fili cewa, duk mutanen Jamhuriyar Jama'ar Sin sun kasance daidai a gaban dokoki. Yayin da ake aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa, wasu al'amuran rashin da'a sun auku, amma ko wane ne idan ya yi laifi, to, za a yanke masa hukunci bisa dokoki, ta haka an kare doka sosai."
An bude taron kasa da kasa na 22 kan dokoki ne a birnin Beijing ran 5 ga wata, kuma za a rufe shi a birnin Shanghai a ran 9 ga wata. Bayan taron za a bayar da "Sanarwar Shanghai". Babban taken taron nan shi ne "dokoki da zaman jituwar jama'a a kasa da kasa", wakilai sama da 1500 da suka fito daga kasashe da shiyyoyi sama da 60 sun hallarci taron nan. (Halilu)
|