Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-06 18:04:57    
An bude taron shekarar 2005 na dandalin yin jawabai kan karni na 21 a birnin Beijing

cri
Ran 5 ga wata, an bude taron shekarar 2005 na dandalin yin jawabai kan karni na 21 a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Babban taken taron nan shi ne " neman samun ci gaba mai dorewa tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya aika wa taron sakon taya murna, firayim minista Wen Jiabao na kasar kuma ya halarci bikin bude taron, kuma ya yi jawabi. Dukansu biyu sun bayyana cewa, kasashe daban daban sun yi tattaunawa mai zurfi akan manufar neman samun ci gaba mai dorewa, wannan yana da matukar muhimmanci, kasar Sin tana son ba da taimakonta yadda ya kamata wajen neman samun ci gaba mai dorewa a duniya.

Taron dandalin yin jawabai kan karni na 21 shi ne babban taron kara wa juna ilmi da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ta gabatar da shawara a kan yinsa. An taba shirya irin wannan taro ne a shekarar 1996 da ta 2000. Shahararrun 'yan siyasa da shahararrun kwararru sama da 200 wadanda suka fito daga kasashe daban daban sun halarci taron nan na kwanaki uku don yin tattaunawa a kan babban take na "neman samun ci gaba mai dorewa tsakanin Sin da sauran kasashen duniya". A cikin sakonsa na taya murya, shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, kasar Sin tana ba da matukar muhimmanci ga neman samun ci gaba mai dorewa, kuma ta gabatar da manyan tsare-tsaren samun ci gaba mai dorewa a fili, kuma tana aiwatar da su a tsanake.

Yayin da firayim minista Wen Jiabao ke yin jawabi a gun taron, ya nuna cewa, "ana bunkasa tattalin arzikin duniya cikin rashin daidaituwa, gibin da ke tsakanin arewa da kudu na kara habakawa, talauci da cututtuka da kuma jahilci suna galabaitar da kasashe matasa da yawa, haka kuma sabane-sabane da aka gamu wajen kare muhalli da neman samun bunkasuwa suna da tsanani. Sabo da haka wajibi ne, kasashe daban daban su bi hanyar gaskiya, su nace ga yin kokari ba tare da kasala ba don neman samun ci gaba mai dorewa."

Bayan haka firayim minista Wen Jiabao ya kara da cewa, yanzu, kasar Sin ta gabatar da ra'ayinta a fili dangane da neman samun ci gaba cikin daidaituwa kuma daga dukkan fannoni, kuma ta gabatar da babban aikinta na raya zaman gurguzu mai jituwa tsakanin al'umma. Kasar Sin tana cike da imani ga abubuwan da za su wakana a nan gaba. Ya ce, " muna neman samun bunkasuwa bisa bukatu da ake yi a kasar Sin. Mu gaggauta kyautata tsarin tattalin arziki, mu yi kokari sosai wajen bunkasa harkokin tattalin arziki cikin tanadi kuma ba tare da kazantar da muhalli ba, mu kara daga matsayinmu na yin kirkire-kirkiren kimiyya, mu mayar da aikin ba da ilmi bisa matsayi mai rinjaye, mu kara mai da hankali ga tabbatar da zaman jituwar jama'a da zaman daidaici, ta yadda duk jama'ar kasa za su ci gajiyar sakamako da aka samu wajen yin gyare-gyare da raya kasa."

Haka zalika firayim minista Wen Jiabao ya ci gaba da cewa, hanyar da kasar Sin ke bi wajen raya zaman gurguzu ta zamani ita ce hanyar neman samun bunkasuwa cikin lumana. Ya ci gaba da cewa, "a kafa sabon tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci da gaskiya, wannan babban tabbaci ne ga samun ci gaba mai dorewa. Kasashe daban daban suna da ikon zaben hanyar da za su bi wajen neman bunkasa harkokin tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a bisa halin da suke ciki, ya kamata a kara karfin hadin guiwar duk duniya yayin da ake neman samun ci gaba mai dorewa, kuma kamata ya yi, kasashe masu sukuni su kara daukar nauyi iri na duniya a wuyansu."

A karshen jawabinsa, firayim minista Wen Jiabao ya ce, kasar Sin tana daya daga cikin babban iyalin duniya, tana son ba da taimakonta yadda ya kamata wajen neman samun ci gaba mai dorea. (Halilu)