
Wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto ya bayyana cewa, daga ran 5 ga watan da asuba, bi da bi ne jiragen sama masu dauka fasinjoji na yankin Taiwan sun tashi daga birnin Taibei har sun ketare sararin sama na babban yankin kasar Sin don zuwa birnin Paris da Abuzabi. Ofishin jiragen sama masu dauka fasinjoji na babban yankin kasar Sin ya nuna yarda ga kamfanonin jiragen sama masu dauka fasinjoji guda hudu na yankin Taiwan da su iya ketare sararin sama na mahaifa, wannan shi ne karo na farkon da aka yi.
Wato daga ran 5 ga watan da karfe zero, kamfanonin jiragen sama masu dauka fasinjoji da kayayyaki guda hudu na yankin Taiwan sun iya ketare sararin sama na babban yankin kasar Sin, Bayan da jiragen sama na yankin Taiwan su sami izni ketare sararin sama na babban yanki, za a iya yin tsimin man fetur da lokacin tafiye tafiye da kudin yin gyare gyare.(Dije)
|