Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-02 18:34:47    
Kasar Sin ta bayar da takarda mai suna Kokarin da kasar Sin ta yi a wajen sarrafa soja da kwance damara da hana yaduwar makaman nukliya

cri
A ran 1 ga watan Satumba majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da wata takarda mai suna Kokarin da kasar Sin ta yi a wajen sarrafa soja da kwance damara da hana yaduwar makaman nukliya. A cikin takardar nan an bayyana manufa da ra'ayi na gwamnatin kasar Sin a wajen sarrafa soja da kwance damara da hana yaduwar makaman nukliya, kuma an bayyana yadda kasar Sin ta shiga aikin sarrafa soja da kwance damara da hana yaduwar makaman nukliya na kasashen duniya. Takardar nan ta nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari a wajen sa kaimi ga aikin sarrafa soja da kwane damara da hana yaduwar makaman nukliya, har abada ba za ta kafa daular tasku ba, kuma za ta tsaya tam tam a wajen kiyaye zaman lafiyar duniya da samun ci gaba tare. Yanzu sai ku saurari labarin da aka ruwaito mana.

Wannan takarda ta bayyana ra'ayi da manufa na kasar Sin na sarrafa soja da kwance damara da hana yaduwar makaman nukliya a fannin halin da a ke ciki a wajen zaman lafiya da sarrafa soja an kasashen duniya da babbar manufar kasar Sin da aikin halartar aikin sarrafa soja da kwance damara na kasashen duniya da yin kokarin kwance damara na kasa da shiyya da aikin hana yaduwar makaman nukliya na kasashen duniya. Takardar nan ta bayyana sakamakon da kasar Sin ta samu a wannan fanni, kuma ta gabatar da hakikanan shawarwari.

A gun taron manema labarum da aka shirya a ran nan, Zhang Yan, shugaban sashen sarrafa soja na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya ce, Kullum kasar Sin ta ke tsayawa kan manufar harkokin waje ta 'yancin kai da zaman lafiya, ta tsaya tam tam a wajen bin hanyar zaman lafiya da samun ci gaba. A wajen sarrafa soja da kwance damara da hana yaduwar makaman nukliya kasar Sin ta yi kokarin bin ka'idar amincewa juna da moriyar juna da zaman daidaici da taimakon juna don yin kokarin shimfida kwanciyar hankali da kiyaye zaman lafiyar duniya don samun ci gaba tare.

Takardar nan kuma ta bayyana aikin da kasar Sin ta yi a wajen halartar aikin sarrafa soja da kwance damara da a ke yi a kasashen duniya, ciki har da hana muggan makamai.

Zhang Yan ya nuna cewa, Tun daga rana ta farko da ta samu makaman nukliya ne gwamnatin kasar Sin ta bayar da sanarwar gaske cewa, a ko wane lokaci kuma cikin ko wane hali kasar Sin ba za ta zama ta farko a wajen yin amfani da makaman nukliya ba, kuma ba za ta yi amfani da makaman nukliya ga kasashe da jihohin da ba su da makaman nukliya ba. Kasar Sin ta yi hakuri sosai kan maganar makaman nukliya, kuma kasar Sin ba za ta shiga gasar kera makaman nukliya da a ke yi ba.

Ban da haka kuma takardar nan ta yi bayani kan yadda kasar Sin ta nuna himma a wajen halartar aikin da kasashen duniya ke yi don hana yaduwar makamai. (Dogonyaro)