Gwamnatin kasar Sin ta kira taron ayyukan ba da taimako wajen raya kananan kabilun da ba su da mutane da yawa a Litinin na wannan mako. Wani jami'in da abin ya shafa na kwamitin harkokin kabilu na kasar Sin ya gaya wa kafofin yada labaru a ran 30 ga watan nan cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta rubanya karfinta na gina muhimman kayayyaki da horar da mutane da kuma harkar kudi, don kara saurin raya kananan kabilun da ba su da mutane da yawa. To, kun ji labarin da wakilinmu Tai Linzhen ta ta ruwaito mana:
Kasar Sin wata dinkuwar kasa ce mai yawan kabilu. Ban da kabilar Han da ke samun rinjaye, akwai kananan kabilu guda 55, a cikinsu akwai kananan kabilu guda 22 ne da yawan mutanensu ba ya kai dubu dari, wato kananan kabilun da ba su da mutane da yawa. Ya zuwa yanzu mutanen wadanan kananan kabilu da yawansu ya kai rubu'i suna fama da karancin abinci da tufafi, a wasu kauyuka ma babu wutar lantarki da babbar hanya.
Mataimakin darektan kwamitin harkokin kabilu na kasar Sin Yang Jianqiang ya ba da karin haske cewa, yanzu kwamitin harkokin kabilu na kasar da kwamitin kula da raya kasa da yin kwaskwarima na kasar da ma'aikatar kudi da bankin kasar na tsakiya sun yi nazari da tsara , ta tsara shirye-shirye kan ayyukan raya wadannan kabilu daga duk fannoni.
Yang Jianqiang ya bayyana cewa, 'gwamnatinmu za ta kara karfin gina muhimman kayayyaki da kyautata zaman rayuwa da ayyuka da tsare-tsaren tattalin arziki da sa kaimi kan kara samun kudin shiga da bunkasa harkokin zamantakewar al'ummar kasar da sa kaimi kan ciyar da zamantakewar al'ummar kasar gaba da kara karfin horar da mutane da kuma inganci yawan mutane.'
Ya zuwa yanzu 'yan kananan kabilun da ba su da mutane masu yawa da yawansu ya kai dubu dari 2 suna fama da karancin abinci da tufafi. Game da wannan kuma, Mr. Yang ya ce, gwamnatin kasar Sin tana sa kaimi kuma goyi bayan hukumomin kudi da su kara karfin ba da basussuka ga kananan kabilun da ba su da mutane masu yawa wajen gina muhimman kayayyaki. Sa'an nan kuma, gwamnatin kasar za ta ba da taimako ga wadannan kananan kabilu da su yi amfani da albarkatunsu da ciyar da sana'o'in musamman gaba, ta yadda za a kara kudin shigar da al'ummar wurin suka samu.
Tare da raya tattalin arziki a wurin, gwamnatin kasar ta kara kiyaye al'adun wadannan kananan kabilu, tana kiyaye da girmama harsunansu da kalamominsu da al'adun gargajiya da kuma ikonsu na bin addinai, tana kuma kubutad da kiyaye kayayyakin al'adu na tarihi da ke bakin mutuwa na wadannan kananan kabulun da ba su da mutane masu yawa, haka kuma tana himmantu ga bunkasu al'adun kananan kabilu.
'Yar kabilar Hezhe da ke daya daga cikin kananan kabilun da ba su da mutane da yawa You Jianhong ta bayyana cewa, a cikin shekarun da dama da suka wuce, gwamnatin kasar ta ba da goyon baya sosai wajen raya tattalin arzikin wurin ta hanyar kudi da manufofi, ban da wannan kuma, ta yada da al'adu ta hanyoyi daban daban.
'Don kubutad da daidaita al'adun kabilar Hezhe, karamar hukumarmu ta Tongjiang ta yi amfani da kudin da yawansa ya kai yuan miliyan 4 wajen gina gidan kayan gargajiya na kabilar Hezhe na farko. Sa'an nan kuma, ta kafa kungiyar mawaka da masu rawa ta kabilar Hezhe, wadda ta kan yi mu'amala da kasashen ketare a fannin al'adu. Karamar hukumar Tongjiang ta kuma gina cibiyar horar da yaran kabilar Hezhe da cibiyar nazarin kabilar Hezhe.'
Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin kasar Sin za ta rubanya karfinta na ba da ilmi ba tare da biyan kudi ba a yankunan kananan kabilun da ba su da mutane da yawa, da goyi bayan sa kaimi kan bunkasuwar al'adu da kiwon lafiya a kauyukan wadannan kabilu don inganci zaman rayuwar mutanen wurin.
|